✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar Manajan Kano Pillars Baleriya

An yi jana’izar Manajan Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars Malam Kabiru Baleriya a shekaranjiya Laraba, bayan ya rasu a yammacin ranar Talata a wani…

An yi jana’izar Manajan Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars Malam Kabiru Baleriya a shekaranjiya Laraba, bayan ya rasu a yammacin ranar Talata a wani asibiti mai suna Doctor’s Clinic da ke Bompai, a birnin Kano.

A ranar Talata ce  wata sanarwa da kulob din ya fitar ta ce, Baleriya ya rasu yana da shekara 57, kuma ya rasu ya bar matarsa da ’ya’ya shida.

“Marigayi  Baleria ya taba buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasa kwallo. Sannan ya taba horar da kungiyoyin kwallon kafa na kasa da ’yan shekara 17 da kuma ’yan kasa da shekara 20. Baleriya ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya,” inji sanarwar

Masoya kwallon kafa da dama sun yi ta tururuwa zuwa gidansu da ke Durumin Zungura, a birnin Kano don yi wa iyalansa da ’yan uwansa ta’aziyyar rashinsa.

Baleriya dai ya taba zama Kocin Kano Pillar na wucin gadi kafi daga bisani ya zama Manajan kungiyar.