✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi kira ga mata su lura da alamun cutar kansar mahaifa

A daidai lokacin da ake ci gaba da bikin makon Cutar Kansar Mahaifa, wato cervical cancer, inda ake amfani da makon domin wayar da kan…

A daidai lokacin da ake ci gaba da bikin makon Cutar Kansar Mahaifa, wato cervical cancer, inda ake amfani da makon domin wayar da kan mutane kan cutar, cibiyar wayar da kan al’uma kan kiwon lafiya ta Qaloon Health Support ta yi kira da a rika lura da alamun cutar tare da saurin zuwa asibiti.

Cibiyar ta ce cutar ta kansar mahaifa tana daya daga cikin cutukan kansa da suke addabar al’umma

“Ita dai wannan kansa ta mahaifa akwai wata kwayar cuta da ake kira ‘Human Papiloma Virus’ (HPV) da ke jawo shi, kuma ana daukar wannan  ne mafi akasari ta hanyar jima’i ko saduwa.

Da zarar kwayar ta shiga jiki sai ta taru a qasar mahaifa, amma ba zai janyo wani ciwo ba saboda garkuwar jiki na aiki. amma idan ta taru kuma ta dade a cikin jiki sai ta haifar da kansar.”

Cibiyar ta kara da cewa daga cikin alamun cutar akwai zubar jini da ba na al’ada ba da yawan jin zafi lokacin saduwa da sauransu.

A karshe cibiyar ta Qaloon Health Support ta yi kira ga mutane a rika saurin zuwa asibiti domin gwaji, sannan ta ce a rika yin ragakafin kamuwa da cutar domin, “rigakafin wanan cuta ya fi maganinta sauki, kuma gara a kiyaye kamuwa da ita akan a nemi magani bayan an kamu.”