✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi rabon zakka a Gundumar Dutse

Maskinai da fakirai da malaman addini ne suka amfana da zakkar shanu da kayan amfanin gona da kudade a Karamar Hukumar Dutse da ke Jihar…

Maskinai da fakirai da malaman addini ne suka amfana da zakkar shanu da kayan amfanin gona da kudade a Karamar Hukumar Dutse da ke Jihar Jigawa.

Hakimin Dutse Alhaji Jamilu Basiru Sunusi ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Asabar da ta gabata, a kofar fadarsa,  lokacin da yake raba wa mabukata zakkar.

Ya ce a bana masarautarsa ta raba zakkar gero dami 1,082  da dawa dami 613 da buhu 29 na gyada da buhu 32 na wake da shinkafa buhu 168 da kuma masara buhu 28.

Kamar yadda ya ce, an raba zakkar ce ga fakirai da maskinai da malaman addini, inda fakirai 407 da maskinai 1,772 da kuma malamai 61 suka amfana. “Yawan wadanda suka amfana sun kai mutum 3,053. Akwai wani attajiri mazaunin Kano da ya kawo wa karamar hukumarmu zakkar Naira miliyan daya don rabawa ga mabukata a yankin,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa masarautarsa ta raba zakkar kudi ga mabukata da ke yankin har Naira miliyan 3 da dubu 719 da 75. Ya ce sun samu filayen wakafi guda biyu, wadanda za su yi amfani da su wajen gina masallatan Juma’a da makarantun Islamiyya, duk a gundumarsa ta Dutse.

Da yake nasa jawabin, mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya ce Gundumar Hakimin Dutse ita ce ta zo ta daya wajen samar da zakka mafi yawa a masarautarsa ta Dutse, sai Fagam ta mara mata baya, sai Gundumar Aujara ta zo ta uku.

A jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Dutse, Bala Yakubu ’Yargaba ya ce saboda yadda jama’a suke kula da fidda zakka a masarautar ta Dutse, an samu raguwar sace-sace a masarautar. Ya yaba wa masarautar a kan namijin kokarin da take yi wajen sanya masu sukuni su fitar da hakkin Allah.