✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi ruwan duwatsu ga Mukaddashin Gwamnan Jihar Zamfara

Mukaddashin Gwamnan Jihar Zamfara kuma Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Sanusi Garba Rikiji da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Ahmad Ibrahim da sauran manyan jami’an…

Mukaddashin Gwamnan Jihar Zamfara kuma Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Sanusi Garba Rikiji da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Ahmad Ibrahim da sauran manyan jami’an tsaron jihar sun tsallake rijiya da baya, sakamakon ruwan duwatsu da jama’a suka yi musu a fadar Sarkin Birnin Magaji Alhaji Ahmad Umar dangaladima da ke jihar.
Wannan al’amarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da Mukaddashin Gwamnan da Kwamishinan ’Yan sanda suka je Birnin Magaji da ke karamar Hukumar Birnin Magaji a jihar, don jajanta wa jama’a kisan da wasu barayi suka yi wa jama’ar garin da kuma wasu Fulani da jama’a suka kashe bisa zargin barayi ne.
Jama’ar garin ne suka zargi wasu Fulani uku cewa barayi ne, bayan sun gan su da asuba za su je wani kauye inda suka kashe su, suka kone. Kashe mutanen ya jawo Fulani suka dauki fansa, sai fada ya kaure tsakanin Fulani da Hausawan Birnin Magaji.
Lokacin da Mukaddashin Gwamnan ya je garin bayan gabatar da jawabinsa, sai ya bayyana tallafin gwamnati na Naira miliyan daya da rabi da buhunan hatsi 20 don a ba ’yan uwan Fulanin da aka kashe tare da neman a yi musu addu’a.
Majiyarmu ta ce lokacin da Mai martaba dan Alin Birnin Magaji yake maida jawabi ya ce a matsayinsa na uba ba zai iya gabatar da wannan sako ba, domin ba Fulani kadai aka kashe ba, akwai mutane da yawa da barayi suka kashe. Don haka sai dai idan gwamnati za ta maida wa wadanda aka kashe da wadanda aka yi wa sata hakkokinsu, idan kuwa ba haka ba, sai dai ya ajiye rawaninsa.
Da jama’a suka lura da abin da ke faruwa sai suka hasala, suka shiga yi wa Mukaddashin Gwamnan da Kwamishinan ’Yan sanda ihu da ruwan duwatsu, wanda ya jawo farfasa musu motoci har ma da motar sakataren masarautar. Nan da nan jami’an tsaro suka yi gaggawar bude wuta, ta harbin kan mai uwa da wabi suka harbi mutun hudu. Cikin wadanda suka harba akwai Yahuza Abubakar da Habibu Yakubu da Bello Makau da Muhammad Boy, wadanda a lokacin hada wannan rahoto suke jinya a Asibitin Birnin Magaji, sai daya daga cikinsu da aka kai shi Kano saboda rauninsa ya yi tsanani.  
Mai martaba dan Alin Birnin Magaji ya gudu ya bar garin don gudun abin da zai biyo baya.