Da Dumi Dumi

An yi sulhu tsakanin Babban Bankin Najeriya da Kamfanin MTN

Ministar Kuxi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed

Kamfanin Sadarwa na MTN ya sasanta da Babban Bankin Najeriya, inda ya amince ya biya wasu kudade wadanda suka yi kasa sosai da yadda aka yi tsammani.

Babban bankin ya umarci kamfanin na  kasar Afirka ta Kudu ya mayar da Dala biliyan takwas da hukumomi suka ce ya fitar daga Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Sai dai bayan kwashe tsawon watanni ana kwan-gaba-kwan-baya, daga bisani bangarorin biyu sun amince da biyan Dala miliyan 53 kwatankwacin Naira biliyan 20 kasa da kashi daya cikin 100 na tarar da aka yi masa tun farko kamar yadda BBC ya ruwaito.

A cikin wata sanarwa, Kamfanin MTN ya ce Babban Bankin Najeriya ya yi bitar karin wasu bayanai kafin ya yanke shawarar cewa ba sai ya biya tarar farkon ba.

Dala miliyan 53 ta shafi wata hada-hadar kudi Dala biliyan daya da MTN ya yi ne a shekarar 2008, inda Babban Bankin ya ce an yi abin ba tare da samun amincewar karshe ba.

ADVERTISEMENT

Sai dai, har yanzu, kamfanin na ci gaba da shari’a da gwamnati kan harajin Dala biliyan biyu da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Najeriya ya ce sai ya biya a watan Satumba.

Yadda lamarin yake tun farko

Tun farko dai Najeriya ta kakaba wa Kamfanin MTN harajin Dala biliyan biyu wanda ya kai kimanin Naira biliyan 612, inda a lokacin ya yi ’yan kwanaki bayan Babban Bankin ya ci kamfanin tarar Dala biliyan 8 wato kimanin Naira triliyan 2.4.

Sakamakon wadannan matsaloli da MTN ya fuskanta a lokacin har sai da hannayen jarinsa suka fadi da kusan kashi 20 cikin 100 cikin mako guda.

Ministan Shari’ar  a lokacin ya yi lissafin cewa ana bin kamfanin bashin Dala biliyan biyu wato kimanin Naira biliyan 612 na harajin shigo da kayayyaki da kuma biyan kudi ga ’yan kwangila cikin shekara 10 da suka wuce.

Amma kuma a lokacin kamfanin ya musanta adadin kuma ya ce ya riga ya biya Dala miliyan 700 wato Naira biliyan 214.

Shi dai bayannin harajin ya fito ne a cikin wata sanarwar da ta yi karin bayani game da Dala biliyan 8.1 da Babban Bankin Najeriya ya ce an fitar daga kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Babban Bankin ya ce idan MTN ya mayar da kudin da ya fitar daga kasar nan, za a mayar wa kamfanin kudin da takardar kudin kasar nan wato Naira.

Haka kuma a shekarar 2015 Hukumar Harkoki Sadarwa ta Najeriya ta ci tarar kamfanin na kasar Afirka ta Kudu Dala biliyan biyar domin kin bin umarnin gwamnati na katse layukan mutum miliyan biyar da ba a yi musu rajista ba.

Daga baya kuma sai aka rage tarar zuwa Dala biliyan 1.7.

Fiye da ’yan Najeriya miliyan 50 ne ke amfani da MTN, kuma kashi 30 cikin 100 na harkar cinikayyar kamfanin na gudana ne a Najeriya.

Bankunan da aka ci tara saboda taimaka wa MTN tsallake biyan haraji

Haka kuma, Babban Bankin Najeriya din ya ci manyan bankuna hudu tarar Dala miliyan 16 kimanin Naira biliyan biyar da miliyan 800 bayan an zarge su da taimaka wa Kamfanin MTN fitar da kudi daga kasar ba bisa ka’ida ba.

Sannan kuma an ba bankunan da kamfanin MTN umarnin mayar da kudaden.

Bankunan da aka ci tarar sun hada da Standard Chartered Bank da Stanbic IBTC da Citibank da kuma Diamond Bank.

An fara bincike a kan kamfanin bisa zargin karya dokar musayar kudi ce tun a shekarar 2016, amma daga baya Majalisar Dattawa ta wanke shi daga laifi.

Dokokin Najeriya sun yarda a fitar da kudade daga kasar, amma bisa wasu sharudda.

A lokacin da yake mayar da martani a wancan lokacin, MTN ya zargi Babban Bankin Najeriya da karya wa masu zuba jari gwiwa.

A sanarwar da MTN ya fitar, ya ce Majalisar Dattawa ta binciki zargin fitar da kudin da aka yi wa kamfanin kuma ta gane cewa kamfanin “bai hada baki ba wajen karya dokokin musayar kudade.”

Sanarwar ta kara da cewa MTN kamfani ne mai biyayya ga doka, kuma zai kare kansa.

“Abin takaici ne cewa wadannan al’amura sun sake kunno kai domin za su karya wa masu zuba hannun jari gwiwa, kuma za su iya dakile habakar tattalin arzikin Najeriya,” kamar yadda sanarwar MTN ta bayyana a baya.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya