Da Dumi Dumi

An yi taron tunawa da marigayi mawaki Narambada

Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya ta Jami’ar Bayero da ke Kano ta yi wani babban taro don girmama shahararren mawakin Hausa marigayi Ibrahim Narambada kan gudunmuwar da ya bayar a fagen waka.

A ranar Litinin da ta gabata ce Narambada ya cika shekara 56 da rasuwa, kuma a ranar aka fara taron har zuwa ranar Talata.

Duk da tsawon lokacin da aka dauka da rasuwar mawakin, har yanzu masoya wakokinsa na ci gaba da kewarsa, kan haka ne Cibiyar Koyar da Harsunan Najeriya da ke Jami’ar Bayero ta shirya taro kan mawakin.

A lokacin da yake raye mawakin ya cika baki a cikin wata wakarsa cewa, ba zai taba mutuwa ba, kuma koda ya mutu ma, to zai dawo ya ci gaba da rayuwa.

Sai dai masu fashin baki sun fassara hakan da cewa zai ci gaba da rayuwa na nufin za a ci gaba da sauraron wakokinsa kamar yadda BBC ya ruwaito.

ADVERTISEMENT

Shi dai shahararren mawakin sunan mahaifinsa Maidangwale. An haife shi a 1890 kuma ya rasu a 1963 yana da shekara 73 a duniya.

Mahaifinsa Maidangwale dan asalin garin Filinge ne da ke Jamhuriyar Nijar, amma ya zo garin Tubali ya zauna kuma a nan ya auri mahaifiyar Narambada.  Maidangwale kuma shahararren dan dambe ne a lokacin rayuwarsa.

An haifi Narambada a garin Tubali kuma a nan ya yi karatu, ya yi rayuwarsa duka.

Mahaifiyar Narambada kuwa makidiya ce, don haka a iya cewa ya yi gadon kida ne daga wurinta.

Ya samu sunan Narambada ne dalilin wata karyarsa da ake ce wa Rambada, don haka sai aka yi masa lakabi da Narambada.  Tarihi ya nuna cewa Narambada ya taso ne ya ga kayan kidan kotso a dakin mahaifiyarsa, wanda ita ma na mahaifinta ta yi gado. Kuma ya fara ne da kidan noma.

Wata rana sai ya yi kidan noman kauyensu a Fadar Sarkin Gobir na garin Isa. Da aka ji dadin wakar da kuma yadda yake da kwarewa da hikima, sai aka ka mayar da shi birni ya zamo makadin Gobir.

Don haka ya ci gaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir waka.

Share