Da Dumi Dumi

An yi wa De Klerk tiyata lokacin da Mandela ke jinya

Tsohon Shugaban wariyar launin fata na karshe, De Klerk, wanda ya wargaza tsarin mulkin fararen fata ‘yan tsiraru, ya fitar da Mandela dag kurkuku a shekarar 1990, ya yi fama da jinya, har an yi masa tiyata.
FW de Klerk ya yi fama da jinya a lokacin da yake ko Mandela zai samu sauki, Kafin ya kai wata ziyara kasar Turai, sai kawai ya kamu da rashin lafiya. Wannan tsoho dan shekara 77 ya rika jin hajiyjiya bayan ya dawo daga Turai, don haka ya tafi wajen likitansa.
A shekarar 1994 ya shirya yadda aka gudanar da zaben kasa, inda Nelson Mandela ya smau nasarar zama Shugaban bakar fatar kasar na farko.
A shekarar 1993 aka bai wa Nelson Mandela da FW de Klerka lambar yabo ta Nobel don tabbatar da zaman lafiya.
Jam’iyyar ANC da dimbin masoya sun shirya addu’ar muisamman don neman sauki ga gwarzon mutanen kasar, Nelson Mandela.
“Tsufan nisan shekaru albarka ce,” inji Sakataren ANC, Gwede Mantashe, a jawabibn da ya yi wa dimbin mutanen da suka taru a hedkwatar jam’iyyar.

Share