Da Dumi Dumi

An yi wa direban tanka da yaron mota kisan gilla a Bauchi

Marigayi Abbas Umar Adam da Marigayi Usman Muhammad Auwal
Marigayi Abbas Umar Adam da Marigayi Usman Muhammad Auwal

Wadansu mutane da ake zargin barayi ne, suka yi wa wani direban tankar dakon mai ta kamfanin mai na Zira Oil, mai suna Abbas Umar Adam da yaron motarsa mai suna Usman Muhammad Auwal kisan gilla a garin Magama Gumau da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan yadda lamarin ya faru, Manajan Sufuri na Kamfanin Zira Oil, Alhaji Ali Zira ya ce tankar da aka kashe direbanta da yaron motarsa ta kamfaninsu ce, kuma motar ta taso ne daga Fatakwal dauke da mai, za ta kai Gombe.

Ya ce da suka isa garin Jos sun tsaya a gidan man Zira Oil, a ranar Alhamis da karfe 1:00 na rana, sannan ya sallame su da misalin karfe 2:00 na rana bayan ya ba su man da zai zuba a motar, domin su tafi   Gombe.

“Da direban ya isa Magama Gumau sai ya tsaya, har zuwa wajen karfe 4:00. Akwai wani direbanmu a garin, sai ya gan shi ya ce masa ya tashi ya tafi, kada dare ya yi. Sai direban ya ce zai tafi daga baya, ya sake zuwa ya sake yi masa magana, shi ne sai ya tashi ya tafi. Amma da ya je gaba da garin, sai ya sake tsayawa, sai wadansu mutane suka kira shi a waya,” inji shi.

Ali Zira ya ce daga nan sai direban, ya bar motar da yaronsa ya hau babur ya dawo garin Magama Gumau. Ya ce yaron motar  ya yi ta jira bai gan shi ba, daga baya sai wadansu mutane suka zo, suka tafi da shi. Tun daga nan, “Ba a ga mota ba, ba a ga direba da yaron motar ba,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya ce ya kira waya ya tambaya kan ko motar ta isa Gombe, aka ce masa ba ta isa ba.  Ya ce ya tuka mota daga Jos don neman inda mota ta shiga, ya bi hanyar Gombe yana duba hanya, amma bai gan ta ba. Daga nan ya dawo Magama Gumau ya kama hanyar Gumau har ya fito ta Saminaka, yana nema amma bai ga motar ba ya dawo Jos.

Ya ce sai ya raba lambar motar ga sauran direbobinsu da abokan arziki kuma ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Toro da Bauchi da Kungiyar Direbobi Tanka ta Jos da Gombe.

Ya ce a ranar Babbar Sallar da ta gabata ce, wani ya kira shi ya tambaye shi lambar motar ya fada masa. Sai ya ce masa ga wata motar tanka da aka gani a Bauchi, hanyar zuwa Ningi amma an rufe lambar motar da fenti.

Ya ce nan take ya kira ’yan sandan Bauchi ya sanar musu da ya je suka duba, sai suka gano motar ce, amma babu man da ta dauko, kuma babu direba da yaron motar, sai ’yan sanda suka dauki mota suka kai ofishinsu.

Ya ce bayan kwana daya ya koma Bauchi ya karbo motar, su kuma ’yan sanda suka ci gaba da bincike. Ya ce jami’an SSS na Bauchi suka kira shi a waya suka ce an gano inda aka sauke man, a Magama Gumau a gidan man Manu Soro. Suka ce ya zo da motar a janye man, ya zo da motar aka janye man aka sake komawa da ita Bauchi.

Alhaji Ali Zira ya ce sun yi matukar bakin cikin kashe su. “Wadannan bayin Allah da aka yi wa wannan kisan gilla marayu ne, yaron motar babu uwa babu uwa. Shi kuma direban babu uba,” inji shi.

Ya ce suna rokon Gwamnatin Jihar Bauchi da ta Tarayya su taimaka a kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki, domin a hukunta su.

Shi ma a zantawar Shugaban Kungiyar Tsaro  ta Danga ta Karamar Hukumar Toro Alhaji Yusuf Abdullahi Magama ya ce wani mutum da ya je yin itace a yamma da garin Magana da ya ji wari ne ya zo ya fada musu.

Ya ce da suka je suka duba sai suka ga gawar yaron motar ce. Shi kuma direban an gano gawarsa ce a tsakanin kauyen Rinji da Magama.  Ya ce an yanka direban ne shi kuma yaron motar murde shi ne aka yi ya mutu.

Alhaji Yusuf Danga ya ce suna aikin sa- kai ne, don haka duk wani mummunan abu ya faru, suna kokarinsu su dakile wannan abin.  Ya ce zuwa yanzu, sun kama  mutum biyu da ake zargi da aikata wannan danyen aiki, da wanda ake zargin shi ya tuka tankar ya kai Bauchi.  Kuma sun mika su ga ’yan sandan Toro.

Ya ce masu laifi suna fakewa da masu yin hira ne suna aikata irin wadannan miyagun laifuffuka, inda ya ce mutane suka tafi gidajensu da kamar karfe 12, ne za a iya gano miyagun da suke aikata laifuffuka.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin babban jami’in ’yan sandan Toro, bai same shi ba. Amma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Kamal Datti  ya tabbatar da samu rahoton faruwar lamarin, kuma ya ce suna ci gaba da bincike.

Share