Da Dumi Dumi

An yi wa magidanci kisan gilla a Nasarawa

Wadansu ’yan ta’adda da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa wani magidanci, mai suna Malam Yahaya Oyoga kisan gilla a garin Amaku da ke Karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa.

Majiyarmu ta ce, an sare shi a kai da wasu sassan jikinsa, an kuma  yanka shi a ciki, an datse hannayensa biyu an raba su da gangan jikinsa, sannan a karshe aka yanke masa mazakuta da  hakan ya yi sandiyar zubar jini ya yi ajalinsa.

Majiyarmu ta ce, magidancin manomin doya ne da dan uwansa ya taba zama Gwamna Jihar, kuma bayan da ya rabu da daya daga cikin matansa hudu, ya fara zawarci  wata bazawara har ya shige gaban wadansu zawarawanta.

Majiyarmu ta ci gaba da cewa, ana zargin wadansu daga cikin zawarawan da ya kasa ko kuma masu aikata miyagun ayyuka ne suka kashe shi.

Bincike ya tabbatar da cewa, ranar da za a yi masa kisan gillar, ya je zawarci a kauyen da bazawararsa take, aka nemi ya kwana a dakin baki a can saboda dare ya yi, amma sai aka yi masa waya  ya amsa ya ce ga shi nan tahowa, kuma ba a san wanda ya yi masa wayar ba.

ADVERTISEMENT

Tuni aka yi jana’azarsa kamar yadda Musulunci ya tanada

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ASP Ramhan Nansel ya ce, ba su samu labarin wannan aika-aika ba, amma za su bincika.

Amma wata majiyar ta ce ana gudanar da binicken ne a boye.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya