✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Nafisa Abdullahi Afuwa- Arewa, MOPPAN

A ranar Litinin da ta gabata ne Kwamitin Gyara Kayanka da ke karkashin kungiyar Arewa Film Makers da MOPPAN da kungiyar daraktoci da kuma ta…

Jaruma Nafisa AbdullahiA ranar Litinin da ta gabata ne Kwamitin Gyara Kayanka da ke karkashin kungiyar Arewa Film Makers da MOPPAN da kungiyar daraktoci da kuma ta dattawa ya yi wa fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi afuwa, inda a yanzu jarumar za ta ci gaba da gudanar da harkarta kamar yadda ta saba.
Isma’il Afakallah, Shugaban kungiyar Arewa Film Makers, kuma daya daga cikin mambobin kwamitin ne ya shaida wa wakilinmu batun afuwar ta wayar salula.
Ya ce: “Kwamitinmu ya zauna da jaruma Nafisa Abdullahi a ranar Lahadin da ta gabata sakamakon takardar ba da hakuri da ta rubuto, bayan ta rubuto ne muka ga yiwuwar zaman, inda kuma muka gayyace ta.”
Ya ce, bayan ta zo ne suka karanta mata laifuffukanta, ba ta yi gardama ba, sannan ta sake ba da hakuri, “ka ga wannan ya nuna cewa a kullum gyara muke son kawowa ba wai rudani ba, mun gargade ta, mun nuna mata babu wanda ya fi karfin doka, kuma duk wani abu mutum zai yi na jama’a dole sai ya yi taka tsan-tsan.
Shugaban MOPPAN Khalid Musa ne ya rubuta takardar yin afuwa, inda kuma ya ce, a kullum fatansu shi ne ’yan fim su gudu tare su kuma tsira tare.
Ya ce: “Ba mu da wani kulli ko kuma mu yi wa wani bita-kulli, mu dai burinmu a gudu tare da tsira tare a wannan masana’anta, domin idan sunanta ya baci, mun baci idan kuma ya gyaru to da mu za a rika dariya.”
A karshe ya nemi a ‘yan  fim su ci gaba da ba kwamitinsu hadin kai, a lokaci guda su rika tsare mutuncinsu da kuma gudun duk wani abu da zai jawo yamididi a cikin gari.
A wannan zaman akwai Isma’il Afakallah da Kamilu Jigon  Hausa da Khalid Musa Shugaban MOPPAN da Falalu dorayi daga kungiyar MOPPAN da kuma ta daraktoci, “duk da cewar sauran ‘yan kwamiti ba su samu damar halarta ba, amma da amincewarsu aka yanke wannan hukuncin.” inji Afakallah
Idan ba za a manta ba dai a kwanakin baya ne kwamitin gyara kayanka ya dakatar da jarumar kan laifin kin amsa gayyatarsa bayan ya tuhume ta da laifin shigar badala da kuma shirya shagulgulan da ba su dace ba.