Da Dumi Dumi

An yi yunkurin hallaka Sakataren marigayi Ado Bayero

Tsohon Sakataren marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, Alhaji Isa Sanusi Bayero ya sha da kyar daga hannun wasdanu mutane da ba a san su wane ne ba, lokacin da suka yi yunkurin hallaka shi.

Mutanen su biyar, an yi zargin ’yan-ina-da-kisa ne da aka dauki hayarsu don su kashe shi, kuma sun mamaye gidansa ne da ke Unguwar Sharada a Kano, suka yi ta harba bindigogi a sama da nufin shiga cikin gidan.

Shi dai Isa Sanusi Bayero wanda ya yi aiki da marigayi Sarki Ado na tsawon shekara 15, Sarki Muhammadu Sanusi II ya  sauke shi daga mukaminsa.

Da yake bayyana yadda al’amarin ya faru, Isa ya ce mutanen su biyar suna dauke da bindigogi sun isa gidansa da misalin karfe 7:40 na dare, inda suka rika tambayar ina yake.

Isa Sanusi wanda kwararren matukin jirgin sama ne kuma ya yi aikin tuka tsofaffin shugabannin kasa biyar da suka hada da Ibrahim Badamasi Babangida da Cif Olusegun Obasanjo da Abudussalam Abubakar da Sani Abacha da kuma Cif Shonekan.

ADVERTISEMENT

“Ina zaune a falona a lokacin da ’yan bindigar suka zo gidana kuma take suka fara harbi a sama. Direbana ya fita domin ya ga abin da ke faruwa. Sai ’yan bindigar suka nuna shi da bindiga a kansa, suka ce ya kai su wurina, inda nake kallon talabijin. Daga bisani sai na bi bayan direban nawa, inda na gan shi tare da daya daga cikin mutanen, yana rike da bidiga. Ni kuma sai na yi sauri na rufe kofa, na koma falo ina kururuwar neman agaji. Daga nan dai sai ’yan bindigar suka gudu ba tare da sun raunata kowa ba,” inji shi.

Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da samun rahoton faruwar al’amarin kuma ya ce sun dukufa wajen bincike.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya