✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zaman sauraren karar Manjo Almustafa

Kotun daukaka kara da Manjo Hamza ya daukaka kara gabanta a kan hukuncin kisa da Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke masa, a ranar Litinin…

Kotun daukaka kara da Manjo Hamza ya daukaka kara gabanta a kan hukuncin kisa da Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke masa, a ranar Litinin ta saurari bangarorin mai gabatar da kara da na mai kare wanda ake karar wato gwamnatin Jihar Legas. Kowanensu ya baza hujjojinsa gaban masu shari’ar su 3, karkashin Mai shari’a Amina Augie, wadda ta maye gurbin Ibrahim S. Alawa, wanda ya janye daga shari’ar kuma bai bayyana wa kowa dalilin yin hakan ba.
Lauyoyin masu gabatar da kara wato masu kare Manjo Almustafa da Alhaji Lateef Shofolahan, sun sake tado da maganar shaidun nan guda biyu wato Mohammed Abdul Katako da Saje Barnabas Jabila, wanda aka fi sani da Saje Rogers. Mohammed Abdul Katako, wanda aka ce shi ya tuka motar da aka bi marigayiya Hajiya Kudirat Abiola aka harbe ta, ya shaida wa kotu, a wani lokaci can baya, cewa ranar da aka kashe Hajiya Kudirat yana garin Azare waje bikin aurensa.
Shi ma Sajen Rogers din ya shaida wa wa kotun cewa an shirya masa ne ya zo gabanta ya yi wa manjon karya, kuma an yi masa alkawarin za a ba shi wasu abubuwa, an ba shi kadan daga cikin alkawarin, sauran kuma shiru yake ji.
Wadannan batutuwan dai su ne suka mamaye daukacin wannan zaman kuma Mai shari’a Amina Augie ta ce yana yiwuwa a ce mutum yana Azare a Jihar Bauci kuma yana Legas duk a rana guda. Ta ce za su ba da hukunci, amma ba za su bayyana kowace rana ba ce, amma za su sanar da bangarorin biyu ta hanyar sako.
daya daga cikin lauyoyin masu kare Manjo Almustafa, Mista Joseph Dauda ya ce suna fata daga wannan zama ne karshen shari’ar da ta su Almustafa kwashe shekaru 14 a tsare. Lauyan gwamnatin Jihar Legas kuwa cewa ya yi basu da wata sauran magana sai abin da kotu ta yanke
Shari’ar dai mace ce mai ciki, amma kamar sauran shari’un da suka gabata, magoya bayan su Almustafa sun yi dafifi cikin harabar kotun domin nuna goyon bayansu.