Daily Trust Aminiya - An yi zanga-zangar adawa da korar Habashawa daga Saudiyya
Subscribe

An yi zanga-zangar adawa da korar Habashawa daga Saudiyya

Habashawa na zanga-zangar adawa da korar mutanensu daga SaudiyyaBakin hauren Habashawa sun yi artabu da ’yan sandan Saudiyya, hart a kai ga an kashe mutum uku, bayan da aka farmaki Bakin haure ’yan kasar Habasha, har mutum dubu 50 Saudiyya ta kora su8ka koma kasarsu, kamar yadda ma’aiktar harkokin waje ta bayyana a Larabar da ta gabata. A kasar Habashawa kuwa an yi mummunar zanga-zangar nuna adawa da wannan kora a gaban ofishin jakadancin Saudiyya da ke kasar.
Gwamnatin kasar Habasha ta tabbatar da rasuwar ’yan kasarta mutum uku, a yamutsin da aka yi tsakanin ’yan sandan Saudiyya da mutanenta.
“Da mun yi hasashen yawan mutanen a kan dubu 10, amma sai suka yi ta karuwa,” a cewar mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Dina Mufti, kamar yadda ya bayyana wa kamfanin Dillancin Labarai na AFP. Kuma ya bayyana cewa nan gaba yawan Habashawan da za a kora daga Saudiyya zai kai dubu 80.
kasar Habasha ta fara kwashe al’ummarta daga Saudiyya bayan da Sarki Abdullah ya yi musu afuwar wata bakwai, kan su nemi cika ka’idojin zama a kasar, ko kuma nan da ranar  4 ga watan Nuwamba, wa’adin zamansu ya kare.

texem
More Stories