✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zangar adawa da sakin wadanda ake zargi da satar mutane a Adamawa

A ranar Talata ce aka gudanar da zanga-zangar sakin wadanda ake zargi da laifuffukan garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Girei ta Jihar Adamawa. Mazaunan…

A ranar Talata ce aka gudanar da zanga-zangar sakin wadanda ake zargi da laifuffukan garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Girei ta Jihar Adamawa.

Mazaunan karamar hukumar sun nuna bacin rai da rashin gamsuwa kan yadda ake sake wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane, kuma sun dauki alkawarin ci gaba da gudanar da wannan zanga-zangar har sai an fara yin hukuncin da ya dace ga wadanda ake zargi.

Daya daga cikin masu zanga-zangar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Sau da yawa ana kama wadanda ake zargin da satar mutanen amma sai a ga sun dawo suna yawonsu kamar ba su aikata komai ba.

Yin garkuwa da mutane yanzu ya zama wata harkar kasuwanci.Ganin haka ne ya sanya muke zargin cewa masu garkuwar za su iya sayen ’yan sanda da alkalai wajen rashin hukunta su. Idan ba a farga ba, za a iya fuskantar inda doka ba za ta yi tasirin komai ba domin abin ya fara isar mutanen gari,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya ce, “Mun kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane a hanyar Karamar Hukumar Girei tare da hadin kan mambobin ‘Operation Farauta. Wasu laifuffukan da ake zargin mun aika babban ofishinmu sashen gudanar da bincike sannan wasu laifuffukan da karrakin na gaban Kotun Majistare ta 4 a nan Yola.”

“Yin garkuwa da mutane babban laifi ne sannan ba za mu yi wata-wata ba wajen kama duk wanda ake zargi da aikata wannan laifi ba. Ina so in tabbatar muku cewa ’yan sanda ba za su taba hada kansu da masu aikata laifuffuka ba. Za kuma ku iya gudanar da bincike game da wannan domin sanin ainihin lamarin,” inji shi.