Da Dumi Dumi

An zabi sabbin shugabannin Hukumar FA ta Ghana

Kurt Okereku sabon Shugaban Hukumar FA ta Ghana
Kurt Okereku sabon Shugaban Hukumar FA ta Ghana

Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Ghana (Ghana Football Association- GFA) ta yi sababbin shugabanni bayan shekara daya da rushe shugabannin nata bisa laifuffukan cin hanci da rashawa.

Ranar Juma’ar da ta gabata ce aka gudanar da zaben, inda Kurt Okereku ya zama shugaba bayan ya kayar da abokan hamayyarsa biyu.

A watan Yunin bara ce gwamnatin kasar ta rushe shugabannin hukumar bayan an ga shugabanta na lokacin Mista Kwesi Nyantakyi a wani bidiyo na binciken kwakwaf yana karbar cin hanci daga dan jaridar da ya bad-da-kama a matsayin mai zuba jari.

Dala dubu 65, aka ce ya karba (kimanin Naira miliyan 23). An kafa kwamitin rikon kwarya wanda ya ci gaba da jagorantar hukumar har zuwa lokacin zaben.

Mista Nyantakyi da aka sallama shi ne Mataimakin Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) sannan mamba a Kwamitin FIFA wato FIFA Council.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda Sashsin Hausa BBC ya ruwaito, an bude zaben ne da zaben mutum 120 a fadin kasar, wadanda za su rike mukamai daban-daban a GFA kafin zaben manyan ’yan kwamitin hukumar su 11.

Sabon shugaban zai jagoranci hukumar na tsawon shekara hudu kafin a sake zabe a shekarar 2023.

Wannnan wani babban mataki ne na dawo da martabar kwallon kafa a kasar Ghana bayan waccan badakala da ta faru, musamman wasannin Firimiya na kasar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya