Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An zabi Shugabanni biyu a Majalisar Dokokin Bauchi

An samu rudani game da zaban shugaban majalisar dokokin Bauchi yayin da bangarorin da ke hamayya da juna suka zabi shugabanni daban-daban a zauren majalisa.

Hakan yasa aka ‘yan takarar neman shugabancin majalisar biyu Abubakar Suleiman Ningi da Kawuwa Shehu Damina suka zama shugabannin majalisar.

ADVERTISEMENT

‘Yan majalisa 11 na bangaren Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP sun zabi Alhaji Abubakar Y. Suleiman, wanda dan jam’iyyar hamayya ne ta APC. Sai dai ba shi jam’iyyar ke so ba a matsayin Shugaban majalisar.

Yayin da ‘yan majalisa 20 da ke goyon bayan tsohon gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar suka zabi Kawuwa Shehu Damina a matsayin na su shugaban majalisar.

ADVERTISEMENT

Mambobin jam’iyyar APC guda 22 ne a majalisar, na PDP takwas, yayin da jam’iyyar NNPP ke da guda daya.