Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An zabi shugabannin Kungiyar MOPPAN na Abuja

Wadansu daga cikin sabbin shugabannin Kungiyar MOPPAN reshen Babban Birnin Tarayya Abuja a lokacin da ake rantsar da su.

Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), reshen Birnin Tarayya Abuja ta gudanar da zaben shugabanninta. k

An gudanar da zaben ne a ranar Asabar da ta gabata a Kufaina da ke Dei-Dei a Abuja.

ADVERTISEMENT

Zaben ya gudana ne a karkashin jagorancin Sakataren Kungiyar MOPPAN na Jihar Kano, Malam Salisu Mohammed (Officer) a matsayin Shugaban Kwamitin Zaben da shahararren jarumi kuma furodusa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama a matsayin Sakatare.

Alhaji Habibu Barde, Shugaban riko na kungiyar ne ya zama sabon Shugaban Kungiyar bayan ya yi takara ba tare da abokin hamayya ba, inda Aminiya ta gano cewa Barde ya yi wannan takara ba tare da abokin hamayya ba saboda gudunmawar da ya ba kungiyar a lokacin da yake shugaban riko.

ADVERTISEMENT

A yayin zaben furodusa, Alhaji Bala Kufaina ya samu nasarar zama Mataimakin Shugaban, inda aka zabi Malam Lawan Idris a matsayin Sakatare, sannan marubuci kuma Editan Leadership A Yau, Nasir S. Gwangwazo ya zama Sakataren Watsa labarai na Kungiyar.

Bayan an kammala zaben ne,  an bayyana wadanda suka lashe zaben kuma aka rantsar da su a ranar Lahadin da ta gabata, wato kwana daya bayan  kammala zaben.

Fitattu da tsofaffi da kuma masu ruwa-da-tsaki a masana’antar fim ta Kannywood sun halarci zaben da kuma rantsarwar. A ciki akwai da tsohon Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kasa mai kula Arewa maso Yamma, Dokta Ahmad Muhammad Sarari da tsohon Shugaban MOPPAN na Kasa Malam Abdullahi Maikano da kuma fitaccen Darakta Ishak Sidi Ishak.

Har ila yau Shugabar MOPPAN reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Lamaj da Shugaban Kwamitin Zabe na MOPPAN na Kasa kuma Shugaban Kungiyar a Jihar Neja, Malam Haladu Muhammad sun halarci taron.

Manyan bakin wurin zaben

A yayin da yake jawabi, Sabon Shugaban Kungiyar, Alhaji Habib Barde ya sha alwashin cewa za su ba marada kunya.

Ya ce, “Muna sane da nauyin da aka dora mana, amma insha Allahu za mu ba marada kunya. Ina kuma rokon Allah Ya ba mu ikon sauke nauyin da aka dora mana bisa gaskiya da kuma amana,

“Sannan na gode wa mahalarta taron bisa yadda suka bar ayyukansu suka halarci rantsar da sababbin shugabannin duk da dimbin uzuri da ke gabansu, musamman wadanda suka baro garuruwansu, don shaida taron, wadanda suka hada da shugabannin Kungiyar MOPPAN da ke jihohin yankin Arewa ta Tsakiya da sauran sassan kasar nan, hakan ba karamar karramawa ba ce a gare mu,” inji shi.

Sabon Shugaban ya kuma gode wa mambobin kungiyar bisa kada musu kuri’a da suka yi, “Wanda hakan ke nuni da yadda suka yarda kuma suka amince da mu, don haka ina kara kira gare su da su ba mu hadin kai don mu kai kungiyar ga matakin nasara.”

A yayin jawabin Shugaban Kwamitin Zaben, Malam Salisu Mohammed Officer, ya bukaci sababbin shugabannin su zamo masu rike amana da taka-tsantsan wajen tafiyar da ayyukan kungiyar.

“Ina kira gare ku da ku rike amana da kuma yin taka-tsantsan wajen tafiyar da ayyukan kungiyar, matsayin da kuka hau kai yanzu ba karamin jan aiki aka dora muku ba,” inji shi.

Ofisa ya kuma bukaci sababbin shugabannin su kasance masu adalci ga dukkan ’ya’yan kungiyar.

Ya ce,“Wannan zabe abin farin ciki ne, don haka ku yi adalci a tsakanin dukkan mambobin kungiyar, sannan zan yi amfani da wannan dama wajen nuna farin cikina kan irin hadin kan da kuka ba kwamitina, duk da cewa mun taso ne tun daga wasu jihohin muka zo Abuja, domin gudanar da wannan zabe.”

A jawabin, Dokta Sarari ya ja hankalin shugabannin jihohi na kungiyar MOPPAN da su kasance masu hadin kai don su zama tsintsiya madaurinki daya.

Ya ce, “Ba wai kawai na Abuja kadai ba, hatta sauran jihohi suna bukatar a tafi tare, don fitar da jaki daga duma, kasancewar halin da kasuwancin fim ya tsinci kansa ciki a wannan lokaci dole sai an hada kai kafin a samu maslaha.”

Ya yi kira ga shugabannin Kungiyar MOPPAN su tabbatar da sun tafiyar da shugabanci ta hanyar sauke nauyin da Allah Ya dora musu ta la’akari da bukatun mafi yawan mambobinsu a wajen yanke hukunci kan abubuwan da suka shafi kungiyar a kowane mataki.

Darakta Ishak Sidi gode wa sabon Shugaba Barde da Mataimakinsa Kufaina da sauran mambobin ya yi bisa daukar nauyin dawainiyar taron, “Wannan ba karamin karfin hali ba ne, idan aka yi la’akari da halin matsin tattalin arzikin da a ke ciki a halin yanzu,” inji shi.

 Sabon Shugaban Qungiyar MOPPAN na Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Habib Barde
Sabon Shugaban Qungiyar MOPPAN na Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Habib Barde

Tsohon Shugaban MOPPAN na Kasa, Malam Abdullahi Maikano ya bayyana irin namijin kokarin da ya yi wajen ciyar da kungiyar gaba a cikin shekara biyu da ya shafe yana shugabancinta.

A jawabin Alhaji Hamisu Iyantama ya yi addu’ar Allah Ya ba sababbin shugabannin kungiyar ikon tafiyar da ita a kan tafarki madaidaici.

Ya kuma ankarar da su cewa, “Shugabanci babban nauyi ne, sai kun jajirce sosai a kan gaskiya da rikon amana.”

Sababbin shugabannin Kungiyar MOPPAN reshen Birnin Tarayya Abuja sun hada da:

Habibu Mohammad Barde – Shugaba

Bala Mu’azu Kufaina – Mataimaki

Lawal Idris – Sakatare

Abubakar S. Muhammad – Mataimakin Sakatare

Muhammad T. Finisher – Mai Bincike

Garba Muhammad Bado  – Ma’aji

Mama Balaraba – Jami’ar Jin Dadi da Walwala

Zainab Muhammad – Sakatariyar Kudi

Nasir S. Gwangwazo – Sakataren Watsa Labarai