✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi shugabannin ‘yan kasuwar Jos

Wakilan bangarorin ’yan kasuwa a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato su 262 ne suka zabi shugabannin da za su jagoranci Kungiyar…

Wakilan bangarorin ’yan kasuwa a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato su 262 ne suka zabi shugabannin da za su jagoranci Kungiyar ’Yan Kasuwar Jos inda suka gudanar da zaben a ofishin Kungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Filato da ke garin Jos.

Wadanda aka zaba sun hada da Alhaji Dan’azumi Maigida Ibrahim a matsayin  Shugaba da Tunde Buhari a matsayin Mataimakin Shugaba da Hafizu A. Nakande a matsayin Sakatare da Umar Isma’il a matsayin Sakataren Tsare-Tsare.

Sauran shugabannin da aka zaba  su ne Hajiya Rabi Liman, Mataimakiyar Sakataren Tsare-Tsare da Bashiru Sulaiman Is’hak a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a.

Da yake jawabi a wajen Sakataren Kungiyar  ’Yan Kasuwa ta Shiyyar Arewa Alhaji Najib Abubakar, ya yi kira ga shugabannin da aka zaba su hada kai da wadanda ba su samu nasara ba da sauran ’yan kasuwa gaba daya domin a kai ga nasara.

Ya ce Jos ita ce cibiyar  Kungiyar ’Yan Kasuwar Jihar Filato. Domin  akwai kasuwanni 20 a garin. Don haka idan ’yan kasuwar Jos suka hada kai, ’yan kasuwar Jihar Filato da kasa gaba daya za su samu ci gaba.

A jawabin tsohon Shugaban Kungiyar  ’Yan Kasuwar Jihar Filato, Mista Nelson Sokwaibe, ya ce idan ’yan kasuwa suka hada kai a Najeriya, su ne za su zabi wanda zai shugabanci Najeriya.

Ya ce a rana daya idan ’yan kasuwa suka tafi yajin aiki komai zai iya tsayawa a Najeriya. Don haka ya yi kira ga ’yan kasuwar su tsaya su san darajar kansu.

A jawabin sabon Shugaban Kungiyar Alhaji Dan’azumi Maigida Ibrahim ya ce za su tafi da kowane dan kasuwa a kungiyar, domin kowane dan kasuwa nasu ne.

Ya bada tabbacin cewa za su tsaya wajen ganin sun kwato wa ’yan kasuwar hakkinsu a duk inda aka danne musu, kuma za su hada kai da jami’an tsaro wajen tsare dukiyar ’yan kasuwar da lafiyarsu.