Da Dumi Dumi

An zabi ’yan kwallo uku da za su fafata a Gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya ta bana

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) a ranar Litinin ta zabi ’yan kwallo uku da za su fafata a Gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya ta bana.

’Yan kwallon da za su fafata sun hada da dan kwallon Liberpool na Ingila Birgil Ban Dijk da dan kwallon Jubentus na Italiya Cristiano Ronaldo da kuma dan kwallon FC Barcelona na Sifen Lionel Messi.

Idan za a tuna, a kwanakin baya ne Ban Dijk ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Nahiyar Turai inda hakan ya sa wadansu ke hasashen shi zai sake lashe ta Gwarzon Dan Kwallon Duniya a bana.

Ronaldo ya kai wannan matsayi ne bayan ya taimaki kulob din Jubentus lashe Gasar Serie A ta Italiya da Kofin Kalubale sannan ya taimaki Fotugal wajen lashe Gasar Kofin Nahiyar Turai.

An zabi Messi ne saboda ya taimaki kulob din FC Barcelona wajen lashe Gasar La-Liga ta Sifen sannan shi ya fi kowane dan kwallo yawan zura kwallaye a raga a daukacin Nahiyar Turai a kakar da ta wuce.

ADVERTISEMENT

A ranar 23 ga wannan wata ne za a sanar da wanda ya lashe gasar a Milan na kasar Italiya.

Messi da Ronaldo sun taba lashe gasar sau biyar-biyar.

Share