✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Yusuf Zailani sabon shugaban Majalisar Dokokin Kaduna

Majalisar Jihar Kaduna ta zabi Honarabul Yusuf Zailani mai wakiltar Igabi a matsayin sabon shugabanta. Yusuf Zailani, kafin sabon mukaminsa shi ne mataimakin Shugaban majalisar.…

Majalisar Jihar Kaduna ta zabi Honarabul Yusuf Zailani mai wakiltar Igabi a matsayin sabon shugabanta.

Yusuf Zailani, kafin sabon mukaminsa shi ne mataimakin Shugaban majalisar.

Da yake shugabantar zaman majalisar, akawun majalisar Barista Bello Zubairu ya ce tsohon shugaban majalisar Aminu Shagali, ya yi murabus ne daga mukaminsa.

Ya ce, hakan ne yasa aka nemi ‘yan majalisar da su mika sunan wanda suke so ya maye gurbin Aminu Shagali.

Dan majalisa Suleiman Dabo, wanda ke wakiltar Zariya ne ya bada sunan Yusuf Zailani, sannan kuma Dan Majalisa mai Wakiltar Zankwa Bako Kantiyok ya amince.

Daga nan ne akawun Majalisar ya tabbatar da kujerar ga Yusuf Zailani. Har ila yau kuma majalisar ta zabi Honarabul Muktar Isa Hazo, a matsayin mataimakin shugaban Majalisar.

Honarabul Hazo, shi ke wakiltar mazabar Milgoma da ke yankin Zariya a majalisar.

Bayanai sun nuna cewa, tsohon shugaban majalisar Aminu Shagali zai ci gaba da zuwa majalisar domin gudanar da aikinsa kamar tare da sauran ‘yan majalisun.