✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi Trump da wariyar launin fata

An zargi Shugaban Amurka Donald Trump da nuna wariyar launin fata, bayan wasu sakonni da ya sanya a shafinsa na Tiwita, wavanda a ciki yake…

An zargi Shugaban Amurka Donald Trump da nuna wariyar launin fata, bayan wasu sakonni da ya sanya a shafinsa na Tiwita, wavanda a ciki yake sukar wavansu mata ’yan Majalisar Wakilan Amurka.

Duk da cewa bai ambaci sunayen matan ba, amma ya ce sun fito ne daga kasashen da gwamnatocinsu, “tsabagen bala’i ne,” ya rubuta hakan ne duk da cewa an haifi yawancin wavannan mata ’yan majalisa a Amurka ne.

Mista Trump bai tsaya a nan ba, har ma ya nemi su koma gida wato kasashensu na asali.

Matan huvu ’yan Majalisar Wakilan Amurka da ake ganin Shugaban ya yi wa gugar zana , dukkansu an zabe su a lokacin zaben rabin wa’adi na bara.

Kuma akidarsu ta siyasa ta ra’ayin kawo sauyi, ko gaba-dai gaba-dai ta sa sun yi ta samun sabani da Shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi , musamman a kan manufa ko batun shigi-da-fici.

Vaya daga cikin matan, Ilhan Omar, an haife ta ce a kasar Somaliya, amma kuma tun tana karama aka je da ita Amurka. Sauran ukun kuwa, Rashida Tlaib ’yar Falasvinu ce, sai Ayanna Pressley, ’yar asalin Afirka, sai kuma Alevandria Ocasio-Cortez, ’yar kasar Spain da surki da Afirka.

Dukkan matan guda uku daga cikin huvun, an haife su ne a Amurka, hasali ma ita Alevandria, tazarar mil 12 ne tsakanin mahaifar Donald Trump da inda aka haife ta a New York.

A jerin sakonnin Tiwita da ya rubuta Shugaba Donald Trump ya bayyana gwamnatoci da kasashen da matan na asali, da wavanda suka fi cin hanci da rashawa, wavanda kuma ba su dace ba a duk favin duniya.

Sa’annan ya zargi matan da fita karara suna vaga murya da kwakwazo suna gaya wa ’yan asalin Amurka wai yadda ya kamata su tafiyar da gwamnatinsu.

Gidan rediyon BBC ya ce shugaba Trump ya ce: “Me zai hana su koma, su taimaka a gyara can inda suka samo asali inda abubuwa suka tabarbare, miyagun laifuffuka suka mamaye, suka samu gindin zama.”

Matan huvu dai sun mayar wa Mista Trump martani ta kafar  Tiwita, inda Rashida Tlaib ta kira Trump da Shugaban Kasa marar bin doka wanda shugabancinsa kacokan asara ce.

Shugabar Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosi, ta yi Allah-wadai da kalaman na Mista Trump, tana mai bayyana su a matsayin na kyamar ’yan wasu kasashe.

Matan sun kuma mayar da martani ta hanyar kiran taron  manema labarai, a wani matakin bai-vaya na nuna jajircewa da yin tir da caccakarsu da Shugaba Donald Trump ya yi ta kafar sada zumunta da kuma ta baka.

’Yan Majalisar Wakilan huvu, wavanda dukkansu mata ne kuma ’yan tsirarun jinsi a cewar Ilham Omar ta Jam’iyyar Democrats daga Jihar Minnesota wacce aka haifa a kasar Somaliya kuma ta zama ’yar kasar Amurka, ‘wannan ajandar masu ra’ayin fifita jinsin farar fata ne a kasa.’

Trump ya sake wallafa wasu kalaman adawa a shafinsa na Tiwita, inda ya ce dukkan ’yan majalisar huvu su koma kasashensu da rikici da talauci ya yi musu katutu, duk kuwa da cewa uku daga cikinsu ’yan asalin Amurka ne.

Biyu daga cikin matan wato Ilham  da Rashida su ne Musulmi na farko a Majalisar Dokokin Amurka kuma sun yi kiran a tsige Shugaba Trump.