✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana amfani da kafafan sada zumunta wajen yada karya da haddasa kiyayya- Sarkin Fulanin Legas

Sarkin Fulanin jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado, ya bayyana takaicinsa duba da yadda wasu batagari ke yin amfani da kafafan sada zumunta na zamani wajen…

Sarkin Fulanin jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado, ya bayyana takaicinsa duba da yadda wasu batagari ke yin amfani da kafafan sada zumunta na zamani wajen yada labaran karya tare da rura gaba da kiyayya a tsakanin kabilun kasar nan Sarkin fulanin ya shaidawa Aminiya cewa, biyo bayan shirin nan na Ruga da gwamnatin tarayya ta yi yunkurin yi da farko sai wasu batagari suka yi ta shiga kafafan sadarwa suna yada bayanan karya da farfaganda domin kushe shirin.

“Ni kai na ma sai da aka yi ta yada labaran karya game dani, wai an mayar da ni Babban Sarkin Legas wato ‘Emir of Lagos’, sannan wata kafar ta rubuta labarin wai Gwamnan Legas ya kawo ziyara fada ta, duk sun yi haka ne domin a harzuka jama’ar wannan yanki game da sha’anin ruga, domin wannan hoto da aka yi ta yayatawa wai Gwamna ya ziyarce ni ba hoto ne da aka dauka yanzu ba, an dauke shi ne lokacin da Gwamnan Legas yana yawan yakin neman zabe, inda ya ziyarci fadata domin goyon bayan mu, kuma ni a ranar da kafar tace gwamnan ya ziyar ce ni bana Legas na tafi Abuja, sai ranar Talatar da ta gabata na dawo”. In ji shi.

Sarkin ya kara da cewa, jama’a sun yi wa shirin ruga mummunan fahimta, a maimakon su tsaya su fahimci manufar gwamnati na bullo da shirin, “Mutumin da bai fahimci abu ba ya za a yi ya san amfanin sa ko aka sin haka? Wannan shiri ne da in har aka yi zai kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da manoma, kuma abu mafi mahimmaci shi ne a baiwa ‘ya’yan Fulani makiyaya ilimi, ilimi shi ne mabudi, ilimtar da ‘ya’yan Fulani makiyaya shi ne kashin bayan magance rikicin da ake alakanta su da shi”.