✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da bajekoli a Kano

Kimanin mako guda ke nan da fara gudanar da bikin kasuwar bajekoli a Kano wanda Cibiyar Bunkasa Ciniki da Masana’antu da Ma’adinai da Ayyukan Gona…

Kimanin mako guda ke nan da fara gudanar da bikin kasuwar bajekoli a Kano wanda Cibiyar Bunkasa Ciniki da Masana’antu da Ma’adinai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano (KACCIMA) ta shirya.
Bajekolin na bana wanda aka yi masa taken, ‘Ci gaban kasuwanci ta  hanyar hadin kai,’ shi ne karo na 34.
Alhaji Umar dansuleka shi ne Shugaban wannan cibiyar, ya bayyana cewa bajekolin bana akwai tunanin samun nasara a cikinsa idan aka yi la’akari da irin kamfanonin gida da na kasashen waje da suka shigo wannan kasuwa.
Shugaban ya yi kira ga jama’ar jihar da su yi amfani da wannan dama wajen  fitowa don kulla dangantakar kasuwanci da kasashen waje, kasancewar jihar cibiya ce ta kasuwanci. “Ya kamata jama’ar Jihar Kano su fahimci cewa domin su ake wannan bajekoli, duka wadannan mutane da muka gayyato mun gayyato su ne don mu ga cewa harkokin kasuwanci ya kara habaka a Kano.  Dama Kano ita ce cibiyar kasuwanci a Najeriya ba ma a kasar nan ba, har ma a cikin kasashen Afrika . Ba ma sai don bajekoli ba a kullum baki daga makwabtan Najeriya  iriisu Nijar da Kamaru da Chadi suna shigowa Kano don gudanar da kasuwanci iri daban-daban. Ina kara kiran jama’a da su  shigo filin nan su ga abubuwan da ke kasa’.
A yanzu haka dai kamfanoni da kananan ‘yan kasuwa sun baje hajarsu a runfunan da aka tanada a wannan wuri, sai dai akwai karancin fitowar jama’a zuwa kasuwar, lamarin da jama’ ke danganta shi da halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.
Malam Ahmad Salisu, wani mai sayar da kayan daki, ya bayyana cewa, bajekolin na bana ba kamar na shekarun baya ba ne domin kuwa a tsawon kwanakin da suka yi a kasuwar ba su samu wani cinikin a zo a gani ba. “yau mako guda ke nan da muka kawo kayanmu wannan kasuwa, sai dai babu ciniki sosai, idan aka kwatanta da shekarun baya. Wani lokaci za ka ga mutane suna shigowa amma sai dai su yi kallo kawai.” Inji shi.
Wata mata daga cikin masu sayen kaya da suka ziyarci kasuwar mai suna Ummalkhairi Usman, ta bayyana wa Aminiya cewa ta shigo kasuwar nan da niyyar sayen wadansu kayayyaki, amma saboda yadda farashin kayayyakin yake a kasuwar ya sa ba za ta iya sayen komai a wurin ba. “Gaskiya na zo da niyyar sayen wasu kayayyaki saboda muna tunanin za a samu sauki a farashin kayayyakin idan aka kwatanta da na kasuwa, amma sai ga shi farashin daya ne, wani wurin ma farashin yana so ya fi na kasuwa, wato yadda aka saba saye yau da gobe. Hakan ya sa ban iya sayen komia a kasuwar ba.” Inji ta.