✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da binciken tsige Trump

’Yan kwamitin binciken sirri na Majalisar Wakilan Amurka na shirye-shiryensu na karshe don sauraron bahasi a karon farko a bainar jama’a a kan binciken yiwuwar…

’Yan kwamitin binciken sirri na Majalisar Wakilan Amurka na shirye-shiryensu na karshe don sauraron bahasi a karon farko a bainar jama’a a kan binciken yiwuwar tsige Shugaba Donald Trump.

Cikin shaidun da suka bada bahasi akwai William Taylor, shugaban ofishin jakadancin Amurka a Ukraine da George Kent, Mataimakin Sakataren da ke kula da Ofishin Tarayyar Turai da kuma wasu kasashen yankin Asiya.

Taylor da Kent suna daga cikin jami’an diflomasiyya na yanzu da na baya da kuma jami’an tsaron kasa da suka riga suka ba da bahasi a kebance a ’yan makonnin da suka gabata.

Kwamitocin Majalisar Wakilan sun fidda rubutattun bayanan da jami’an suka yi inda suka ba da cikakken bayani a kan yadda Trump da hadimansa suka hura wa Ukraine wuta a kan ta kaddamar da bincike kan daya daga cikin manyan ’yan adawar Trump a zaben shekarar 2020 daga Jam’iyyar Democrat, wato tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden da dansa Hunter Biden musamman kan ayyukan da suka yi a wani kamfanin Gas na Ukraine da kuma wani batu mara tushe mai cewa Ukraine ce ta yi katsalanda a zaben shekarar 2016, ba Rasha ba, kamar yadda Hukumar Bincken Sirri ta Amurka ta fada.