✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da dambarwar siyasa a kasar Benezuela

Ana ci gaba da dambarwa da nuna yatsa a tsakanin kasar Amurka da ke goyon bayan ’yan hamayyar kasar Benezuela da Shugaban Kasar Nicolas Maduro…

Ana ci gaba da dambarwa da nuna yatsa a tsakanin kasar Amurka da ke goyon bayan ’yan hamayyar kasar Benezuela da Shugaban Kasar Nicolas Maduro da kuma mutanen kasar.

Idan ba a manta ba, mun rawaito yadda kasar ta shiga rudun siyasa bayan  kammala zaben kasar, inda Shugaban Kasa mai ci Nicolas Maduro ya lashe, sai kuma ’yan hamayya suka sanar da shugabansu a matsayin shugaban riko.

Akwai yiwuwar Amurka ta auka wa Benezuela da yaki – Shugaba Trump

Da Shugaban Amurka Donald Trump yake tattaunawa tare da bayanin a kan ganawarsa da Shugaban  Koriya ta Arewa da ake tsammanin za su yi kwanan nan, ya ce za su iya amfani da karfin soji wajen auka wa Benezuela.

Gidan rediyon Turkiyya (TRT) ya rawaito Shugaba Trump a lokacin da yake amsa tambayoyi a tashar CBS ta Amurka kan ko za su aika sojoji zuwa Benezuela sai ya ce, “Tabbas wannan ma wani abin lura ne.”

Shugaba Trump ya ce a watannin baya Shugaban Benezuela Nicolas Maduro ya bukaci ya gana da shi amma ya ki ya amince da haka.

A shirye muke mu kare kasarmu – Sojojin Benezuela

A nasu bangaren kuma, sojojin Benezuela sun fara wani atisaye na kwana 5 domin nuna wa Amurka da kawayenta da ke yankin kwanji da karfin sojinsu.

Atisayen ya zo daidai lokacin da ake tarurrukan cika shekara 200 da bayyanar jagoran kwatar ’yancin kasar daga Spain Simon Bolibar ya yi a Angostura.

Sakamakon atisayen an gudanar da babban taro a sansanin soji na Guaicaipuro da ke Jihar Miranda wanda Shugaban Kasar Nicolas Maduro da Ministan Tsaro, Padrino Lopez tare da sauran manyan kasar suka halarta.

A jawabin da Maduro ya yi ga sojojin ya bayyana manyan manufofin Simon Bolibar na kwatar ’yanci.

Ya ce, sojojin za su ci gaba da atisayen har zuwa 15 ga Fabrairu domin nuna wa Amurka da kawayenta kwanji da kuma nuna musu kasar a shirye take game da duk wata barazana da za su yi mata.

Amurka ce ke kulla makirci a Benezuela– Rouhani

A jawabin Shugaban Kasar Iran Hasan Rouhani game da rikicin, ya zargi gwamnatin Amurka da kulla makirci tare da cin amanar al’ummar kasar Benezuela.

Shugaba Rouhani ya yi wannan jawabi ne lokacin da yake maraba da sabon Jakadan Benezuela a Tehran, Carlos Antonio Alcala Cordones, inda ya bayyana cewa ya bayar da gudunmawa domin kalubalantar makircin Amurka a Benezuela.

Rouhani ya kara da cewa, “Mu muna bayar da gudunmawarmu da goyon baya ga zababben Shugaban Benezuela Nicolas Maduru,” inda ya kara da cewa “Mun yi imani wadannan makirce-makirce ne da ake shirya wa domin haifar da husuma a Benezuela kamar yadda aka yi a baya wannan ma ba zai yi tasiri ba, makiya za su ji kunya.”

A yayin da Rouhani ke zargin Amurka da yunkurin ci gaba da yin kaka-gida a duniya ya kara da cewa, “Amurka na yunkurin kalubalantar al’ummar kasashe da kuma kwace ’yancinsu. Suna yunkurin kwace ’yancin kasashe domin ci gaba da mallakar duniya. Amurka duk sauran manyan kasashe ba ta iya jure musu. Mun ga ire-iren matakan kama-karyarta har ma ga kasashen Rasha, China d na Nahiyar Turai.”

Sabon Jakadan Benezuela a Iran Cordones, bayan ya mika takardar fara aiki ga Shugaba Rouhani ya bayyana cewa kasarsa na daukar hurdarta da Iran da muhimmanci sosai. Ya kara da cewa za su ci gaba da kalubalantar yunkurin Jari-Hujja da kwatar ’yanci kamar kasar Iran “Kawarmu ta gaske ke ci gaba da yi da kuma bayar da gudunmawa a kan hakan,” inji shi.

Ba za mu mika wuya ga Amurka ba – Shugaba Maduro

Dimbin al’ummar kasar sun gudanar zanga-zangar lumana inda suka cika titunan Caracas, Babban Birnin kasar, inda suke nuna goyon baya ga Shugaba Nicholas Maduro dauke da hotuna kamar yadda ya yi kira, amma kuma a wani bangaren wadansu sun fito domin nuna goyon bayansu ga shugaban ’yan adawar kasar.

Shugaban Kasar ya yi wa al’ummar kasar jawabi a kan titin Bolibia, inda ya bayyana cewa a wannan shekarar za a gudanar da zaben ’yan majalisar kasar, ya kuma kara da cewa kofa bude take domin tattaunawa da ’yan adawar kasar, haka kuma ya shaida wa kasar Amurka cewa “Benezuela ba za ta taba mika wuya ba.”

Amurka za ta taimake ni –Madugun ’yan adawa

Madugun ’yan adawar kasar Juan Guaido wanda ya bayyana kansa a matsayin Shugaban Kasa na riko ya yi kiran a ci gaba da w-zanga har sai hakarsu ta cimma ruwa.

Da yake jawabi Juan Guaido ya aike da sako zuwa ga magoya bayansa inda ya shaida musu cewa zai shigo kasar tare da taimakon Amurka a  ’yan kwanakin nan.