Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ana ci gaba da wasan damben gargajiya a Zariya

Ana ci gaba da gasar wasan damben  gargajiya da ake yi a kowane yammaci a filin wasan kwallon kafa da ke Titin Kulob (Club Street) a Sabon Garin Zariya Jihar Kaduna.

Filin damben yana cika makil da ’yan kallo da shahararrun ’yan wasan dambe daga bangarorin Kudu da Arewa da kuma ’yan wasan daga  Guramado. Kuma ’yan wasan da suka fito daga Guramado suna buga wasan dambe da kowane bangare na ’yan wasan.

ADVERTISEMENT

A wani wasa da aka fafata tsakanin Alhaji Huladu Nabacirawa Karami daga bangaran Arewa da Awalu Mai Masaba dan Tudun Jukun, an fafata har sau uku amma ba a samu kisa ba, wanda don haka dole sai dai aka dakatar da wasan baki daya.

Sai wasa na biyu da aka fafata a tsakanin Shagon Yusuf daga Arewa da Shagon Kato Maikarfi daga bangaren Kudu, inda Shagon Yusuf daga Arewa ya kashe Shagon Kato Maikarfi tun a turmi na daya, inda Kato Maikarfi ya yi warwas a kasa saboda bugun da ya sha daga hannun Shagon Yusuf.

ADVERTISEMENT

Bayan kammala wasan, alkalin wasa ya yi wa Aminiya bayani a kan dukan wasannin da cewa wasa ya yi kyau sosai, “Sunana Shamsu Dan Mahauta wanda aka fi sani da an kashe alkalin wasa. To wasa na farko dai babu kisa  kuma an yi har turmi uku kamar yadda wasa ya kasance, haka wasa na biyu wanda Shago Yusuf ya kashe Shagon Maikarfi  a turmi na daya. Don haka shi wasa yake, ka ga yadda Shagon Maikarfi ya yi warwas a kasa saboda bugun da ya sha,” inji shi.