Da Dumi Dumi

Ana iya sake ci tarar Najeriya Dala biliyan 2.3 baya Dala biliyan 9.6 na P&ID

A daidai lokacin da Najeriya ke neman mafita kan tarar da aka ce ta biya Kamfanin P&ID ta Dala biliyan 9.6, akwai yiwuwar a sake  cin tararta Dala biliyan 2.3 kan kwangilar Tashar Wutar Lantarki ta Mambilla.

A watan Agustan bana ne, wata kotun Birtaniya ta Kamfanin  P&ID na kasar Faransa damar kwace kadarorin Najeriya da suka kai Dala biliyan 9.6 saboda yadda aka kasa cika yarjejeniyar da suka shiga na habaka iskar gas, wanda kotun ta ce laifin Najeriya ne.

Sai kuma ga Kamfanin Wutar Lantarki na Sunrise Power and Transmission Company Limited (SPTCL) ya shigar da kara kan yarjejeniyar Tashar Wutar lantarki ta Mambila ta Dala biliyan 5.8, inda ya bukaci kotun ta ba shi damar mallakar kadarorin Najeriya na  Dala biliyan 2.3.

Kamar matsalar P&ID, wadda daga baya aka yi kokarin sulhu da kamfanin ya ci tura, shi ma na SPTCL, kusan haka lamarin yake a yanzu.

Babban Jami’in Zartarwa na Kamfanin SPTCL, Leno Adesanya ya ce abin da ya sa suka shigar da karar shi ne ganin yadda aka mayar da su saniyar ware wajen aiwatar da wasu ayyuka a Ma’aikatar Makamashi, kamar yadda takardar koken da suka aika zuwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osibanjo, da Ministan Makamashi, Babatunde Fashola ta nuna.

ADVERTISEMENT

Adesanya ya ce kamfaninsu ya kashe miliyoyin Dala wajen harkokin hada-hadar kudade da harkokin shari’a wajen tattara kusan Dala biliyan 6 domin gudanar da kwangilar, kuma kamfanin ya sha wahalar gaske saboda yadda, “muka samun kutse.”

Da yake bayani kan batun, Ministan Watsa Labarai, Alhaji Lai Mohammed ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da barazanar kwace kadarorin Najeriya.

“Suna barazanar cewa sun fara tattara kadarorin Najeriya. Muna yin duk mai yiwuwa kuma muna fata za mu samu matsaya wajen dakatar da kwace wannan dukiyar kasa. Gwamnatin Tarayya ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da cewa babu wata dukiyar kasar nan da ta salwanta,” inji shi.

Share