✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kokarin farfado da Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya na fuskantar barazanar durkushewa kamar yadda masu sharhi suke cewa. Masana’antar na fuskantar matsaloli da suka hada da…

Masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya na fuskantar barazanar durkushewa kamar yadda masu sharhi suke cewa.

Masana’antar na fuskantar matsaloli da suka hada da satar fasaha da rashin zuba jari daga masu wadata da kuma rashin kulawar gwamnati, duk da cewa ta shafe shekaru da kafuwa.

Falalu Dorayi wanda babban mai bayar da umarni ne kuma yakan fito a matsayin tauraro a fina-finan, ya shaida wa BBC cewa wannan hasashe na masu sharhi gaskiya ne.

Ya ce a yanzu halin da masana’antar ke ciki ya haifar da karayar arziki da durkushewar jari da kuma rufe wasu kamfanonin shirya fina-finai masu girma.

Jarumin ya ce tun farkon kafa masana’antar sun dogara ne a kan sayar da fina-finansu ta hanyar faifayin CD, “Amma da yake yanzu an samu ci gaban fasaha sosai mutane kusan sun daina kallon fim a CD sai a wayoyin hannu da sauran sababbin hanyoyi.

“Idan a da kana yin kwafin CD dubu 100 to yanzu da wuya ka iya yin dubu 5, kuma ko ka yi ba za su sayu duka ba. Don kana zaune wani zai sauke fim din  a manhajar  Intanet ya aike wa mutum 100 a lokaci daya.

Sannan kuma ko sinima ka kai fim dinka da wahala ka samu riba don kuwa babu sinima  da yawa a Arewa kamar Kudu,” inji Falalu.

Duk da cewa yanzu a duniya an yi ci gaban da dora bidiyo a shafin YouTube kadai na sa wadansu samun makudan kudade da shafin ke biyansu, har yanzu a Masana’antar Kannywood ba a fara cin gajiyar abin sosai ba.

“Ai ko ka dora a Youtube din ba za ka samu irin kudin da zai samar maka riba ba, don wata tashar taka ta Youtube ma idan ba ka da masu kallonta da yawa ai ba wani talla da za ka samu balle har kudi su shigo.

“Sai dai kawai yawan mutanen da ke cikinta da yawan fadada tunani da ake yi to zai iya taimakawa a farfado da ita,” inji shi.