✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ana kyamar mutanen China kan cutar Kurona

Yanzu dai kyamar ’yan asalin kasashen Asiya na ci gaba da yaduwa a kasashen duniya bayan bullar cutar Kurona a kasar China. Rahotanni daga Ostireliya…

Yanzu dai kyamar ’yan asalin kasashen Asiya na ci gaba da yaduwa a kasashen duniya bayan bullar cutar Kurona a kasar China.

Rahotanni daga Ostireliya sun ce wani marar lafiya ya ki ya gaisa da wata likitarsa bisa fargabar kamuwa da cutar ta Kurona.

Jaridun kasar Italiya sun ruwaito a ranar Talata cewa jama’a a birnin Benise sun yi ta yin kaki kan rukunin wadansu ’yan yawon bude-ido ’yan kasar China, yayin da a birnin Turin jama’ar gari suka zargi wadansu iyalai ’yan asalin kasar China da yada cutar ta Kurona.

A birnin Milan kuwa wadansu iyaye mata ne suka yi amfani da shafukan sada zumunta wajen kira ga jama’a su nisantar da ’ya’yansu daga ’yan asalin kasar China su kuma nisanci shagunan ’yan China. A kasar Malaysiya mutane kimanin dubu 500 suka sanya hannu kan wata takarda da ke kira a dauki matakin haramta wa ’yan kasar China shigowa kasar ta Malesiya baki daya.