Da Dumi Dumi

Ana musayar yawu kan sa ’yan sanda su kwato taraktocin da aka ba manoma rance a Bauchi

Ustaz Ibrahim Umar Disina
Ustaz Ibrahim Umar Disina

An fara musayar yawu  tsakanin Gwamnatin Jihar Bauchi da manoma kan yadda ta tura ’yan sanda suka kwaro taraktocin noma da gwamnatin da ta shude karkashin tsohon Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ta ba manoma rance.

Idan za a iya tunawa  a bara wani gwamnatin jihar  ta gayyaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda ya kaddamar da taraktocin noma 500 da gwamnatin ta ce za ta bai wa manoma rance da nufin samar da aikin yi ga matasa ta fuskar aikin gona.

Daga cikin taraktocin guda 40 ne kawai suka isa jihar, kuma tsohuwar gwamnatin ta raba su ga manoma 40 inda kowace karamar hukuma ta samu taraktoci  biyu.

Kamar yadda shirin yake kudin kowace tarakta shi ne Naira miliyan 15 da dubu 850, kuma daga cikin kudin duk wanda ya ci moriyar taraktan zai ba da kashi goma na kudin, inda gwamnati za ta biya kashi 30 sauran kuma za a biya a lokuta daban-daban cikin wata 60. Yarjejeniyar ta nuna dole ne wanda ya ci moriyar ya kasance dan daya daga cikin kananan hukumomi 20 da ke Jihar Bauchi, zai kuma ci moriyar rancen ne bayan shi da gwamnati sun sanya hannu a kan yarjejeniyar karbar rancen.

Aminiya ta gano cewa dukkan mutum 40 da suka ci moriyar rancen da suka hada da sarakuna da malaman addini da wakilan kungiyoyin manoma sun cika wadancan sharudda a tsakaninsu da Ma’aikatar Gona ta Jihar Bauchi kafin suka karbi rancen taraktocin.

ADVERTISEMENT

Sai dai Kwamitin Kwato Dukiyoyin Gwamnati da Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kafa a karkashin Jagorancin Birgediya Janar Marcus Kokko ya yi zargin cewa wadanda suka ci moriyar bashin taraktocin sun ki biyan ko kwabo bayan da suka karba cikin wata 14 da ya kamata a ce sun fara biya. Ya ce kwamitin ya rubuta musu takardu don neman su biya gwamnati ko su dawo da taraktocin a maida musu kudinsu na ajiya kashi goma da suka fara bayarwa.

Jami’in Labarai na Kwamitin Alhaji Umar Barau Ningi, Barden Ningi ya shaida wa Aminiya cewa cikin wadanda kwamitin suka rubuta wa takardar har da wani babban manomi a jihar, Dokta Ibrahim Umar Disina, wanda ya karbi taraktar amma ya ki biya lamarin da ya sa kwamitin ya kai kararsa wajen ’yan sanda.

Barden Ningi ya ce kwamitin ya rubuta wa dukkan wadanda lamarin ya shafa kuma duk sun nuna niyyarsu ta biya, wadansu kuma har sun biya ko sun dauki uzuri na lokacin da za su biya amma Dokta Disina sai ya rubuto musu takarda cewa ba ya da wani kaya na gwamnati a hannunsa da kwamitin zai karba. Ya ce kwamitin ya bi duk matakan da suka kamata don karbo taraktar ko manomin ya biya amma ba su daidaita ba, saboda haka su ka dauko takardar da ya cike na alkawari a tsakaninsa da gwamnati da nufin su kira wadanda suka tsaya masa aka ba shi rance su yi masa magana ko zai tuna. Ya ce da suka kira daya daga cikinsu mai suna Malam Abdurrahman Khalil sai ya ce bai taba sa hannu ya tsaya masa don ya karbi rance tarakta ba.

Wakilinmu ya tuntubi Dokta Ibrahim Disina kan wannan batu inda malamin ya ce wannan al’amari an sa siyasa a ciki domin a lokacin yakin neman zabe ya goyi bayan ’yan takarar Jam’iyyar APC ne ba na wannan gwamnati ba.

Kuma ya dauko takardun da Kwamitin ya rubuto masa guda biyu daya mai lamba BA/COM/REC/SGP&F/I/FIN/1 da aka yi ranan 22 ga Oktoba dauke da sa hannun Birgediya Janar Yake wanda aka ce bai cika ka’idar da aka yi da shi na biyan rance ba, kuma aka ba shi umarnin ya biya kudin da ake bin sa cikin sa’o’i 48 ko ya dawo da tarakta ya karbi kudinsa. A ranar 31 ga Oktoba ya bai wa kwamitin amsar takardarsu a rubuce.

Da kwamitin suka samu takardarsa sai suka sake rubuta masa takarda mai lamba BA/COM/REC/S/GP&F/GEN/B.1 ranar 1 ga Nuwamba 2019.

Shi ma kuma Dokta Disina ya sake bai wa kwamitin amsa ranar 2 ga Nuwamba 2019 inda a cikin takardarsa ya nuna wa kwamitin cewa shi mutum ne mai bin dokoki kuma tsarin da kwamitin ya nemi ya biya bashin yanzu ya saba wa alkawarin da yake da shi da Ma’aikatar Gona wadda ta ba shi rancen kamar yadda yake a sashi na 6,7,da 8 na ka’idar da aka sanya hannu a kanta don ba da rancen.

Malamin ya yi barazanar kai kwamitin kotu domin a yi musu fassarar abin da ye cikin alkawarin da aka dauka kafin a ba shi rancen taraktan.

Yayin da Dokta Disina ke shirin zuwa kotu kwamitin kuwa na jiran matakin da ’yan sanda za su dauka ne kan lamarin.

Wakilin Aminiya ya tuntubi Kakakin Rundunar DSP Kamal Datti Abubakar inda ya ce hakika sun samu takardar koke daga kwamitin suna kuma bincike a kan lamarin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya