✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana neman agajin Gwamnati saboda Tamowa a Gombe

Karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara, yasa ake samun karin yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Gombe, an samu wasu yara…

Karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara, yasa ake samun karin yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Gombe, an samu wasu yara daga kauyen Kurba garin shugaban Majalisar Dokokin jihar Habu Kurba.

A ziyarar da Aminiya ta kai Cibiyar lafiya ta jihar inda ake kira gidan Magani ta ga wasu kananan yara da Iyayen su mata suka kawo su saboda wannan rashin lafiya ta ciwon yunwa da ake basu abincin nan na ‘Ready to Use Therapeutic Food RUTF’, da yake taimaka musu wajen gina su.

Wata majiya ta shaidawa wakilin mu cewa, a wannan gidan Magani anyi watanni hudu babu wannan abincin yara na RUTF wato ‘Ready to Use Therapeutic Food’. Jami’i mai kula da sashin abinci mai gina jiki na Karamar Hukumar Gombe Muhammad H Bawa, ya ce tun ranar 25 ga watan Janairu na wannan shekarar ta 2019 rabon su da RUTF sai a ranar Juma’ar makon jiya 19 ga watan Yuli nan suka samu kaso na karshe.

Wani abu da wakilin mu ya gano a gidan Maganin shi ne wannan (RUTF) da aka basu na karshe a makon jiya din shi ne kason da ake tsammani daga shi babu wanin hakan ya haifar da rashin bada kason kudin gwammnatin jihar ne da yasa asusun kula da kananan Yara na Majalisar dinkin duniya UNICEF janyewa daga shirin samar da abincin yaran na RUTF.

Muhammad H Bawa, ya shaidawa manema labarai da kungiyoyin farar hula CSO da ISMPH, cewa a ranar 22 ga watan nan na Yuli din aka kawo musu katan dari 500 kadai.

Yace wannan katon dari 500 da aka basu ba zai wuce watanni biyu ba a wannan asibiti na gidan Magani saboda ana samun karuwar Yara da suke fama da cutar ta Tamowa da suke zuwa daga ciki da wajen Gombe musamman Yankunan karkara inda aka samu mata biyu a lokaci daya cikin takwas da suka zo daga garin na Kurba.

Har ila yau a gidan Maganin akwai mata da suka kawo ‘ya’yan su allurar rigakafi ba su san yaran na fama da cutar ta yunwa ba, har sai da aka duba su aka tura su sashin karbar abincin na RUTF.