✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana neman ministoci bita-zaizai

A sakamakon sauke ministoci guda tara da Jonathan ya yi a makon jiya, yanzu ana da guraben monistoci guda goma ke nan idan aka hada…

A sakamakon sauke ministoci guda tara da Jonathan ya yi a makon jiya, yanzu ana da guraben monistoci guda goma ke nan idan aka hada da ministan  ma’aikatar bunkasa rayuwar matasa Alhaji Inuwa Abdulkadir  da Jonathan ya fara saukewa kwanakin baya.
Guraben da aka samu a sakamakon sauke ministocin da aka yi ranar Laraba lokacin taron majalisar zartarwa na makon jiya ya kunshi wadansu ma’aikatu masu romo guda uku, watau ma’aikatar ilimi da Farfesa Rukayya Ahmad Rufa’i ta bari, kodayake hasken ma’aikatar ya dasashe a ‘yan kwanakin nan saboda yajin aikin da malaman jami’a suke yi, amma duk da haka tun da wuri ne da ya kunshi hukumomi fiye da ashirin a karkashinsa da jami’o’in gwamnatin tarayya da kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi fiye da dari, wure ne da saboda lagwadarsa ‘yan kwangila ‘yan siyasa na Najeriya za su kamanta shi da cibiyar samar da wutar lantarki na Afan.
Haka kuma ma’aikatar tsaro da Misis Olusola Obada ta bari kwanan nan wuri ne da ‘yan siyasan Najeriya suke matukar sha’awa, musamman a wannan lokacin da rikicin Boko Haram ya kai matuka. Sai dai kuma karfin iskar bam din da masu tayar da kayar bayan suke danawa yake tasarwa na iya yin awon gaba da kujerar ministan, kamar yadda ya faru da gogaggen ma’aikacin gwamnatin nan Dokta Bello Haliru Muhammad a shekarar da ta gabata. Ko babu wannan matsalar ta Boko Haram, aiki a ma’aikatar tsaro yana tattare da matsala, domin sojoji suna yi wa duk wanda aka ba ma’aikatar wanda ba soja ba ne kallon hadarin kaji. Duk da haka ma’aikatar tsaro wuri ne da ‘yan siyasan Najeriya suke kallo a matsayin wata babbar taska, domin kai tsaye ake bayar da kwangila a ma’aikatar ba sai an buga tanda ba. Ko ka taba bude jarida ka ga inda ma’aikatar tsaro take neman wadanda za su sayo mata tankokin yaki samfurin T-84 da jiragen yaki samfurin Alpha? Bayar da kwangila a boye a wurin dan Najeriya kamar korama ce a wurin makiyayin da ke kiwon dabbobi a Hamada.
Haka nan kuma idan burinka mayar da shiga jirgin sama kamar gidanka ne, babu ma’aikatar da ta dace da kai kamar ma’aikatar harkokin waje da Jakada Olugbenga Ashiru ya bari. Ina iya tunawa, a shekarar 2007 lokacin da aka zabi Gwamnan jigawa Sule Lamido kafin a rantsar da shi ya kawo ziyara ofishin Daily Trust inda na tambaye shi ko shi ma zai rika fita kasashen waje akai-akai? Lamido ya fahimci inda tambayata ta dosa, domin an zargi wanda ya gada Saminu Turaki da tarewa gaba daya a kasashen ketare, domin haka sai Lamido ya ce, kasancewarsa wanda ya rike mukamin ministan ma’aikatar harkokin waje na tsawon shekara hudu, duk inda yake son zuwa a duniya ya riga ya tafi, domin haka zai zauna ne ya yi mulkin Jigawa a Dutse. Me yiwuwa a bai wa Saminu Turaki ministan ma’aikatar harkokin waje, idan aka yi haka kuwa an sanya shanshani ke nan ya kula da harkar zirga-zirga.
Na karanta a wata jarida inda wani yake bata lokacinsa yana bayanin cancantar da ya kamata a yi la’akari da ita kafin a nada minista a ma’aikatun da aka sauke ministocin, ina ganin bata lokaci ne yin irin wannan bayanin, domin wanda zai nada ministocin ba abun da ya dame shi ba ke nan, babu shakka Jonathan yana bukatar cancanta, amma ba takardun shedar karatu ko dogayen bayanin cancantar mutum ba. Daga bayanin da aka yi na dalilin sauke ministan matasa da kuma sauran ministocin da aka sauke, ya nuna cewa shugaba Jonathan ya yi haka ne domin wani buri na siyasa kawai. An sauke wadansu ministocin ne domin kusancinsu da wadansu gwamnoni bakwai na PDP, wadansu kuma an sauke su ne domin a samu gurbin biyan bukatun wadansu al’iummomi a wadansu jihohi. Watau dai za a iya cewa an sauke ministocin ne domin a samu wadanda za su iya ja da gwamnonin da suka yi bore.
A takaice dai, shugaba Jonathan ba zai yi la’akari da kwarewa da gogewa ko zurfin karatu ba ne wajen nada ministocin da za su maye gurbin wadanda aka sauke ba, zai yi la’akari ne kawai da wadanda za su zama mijin ta-ce, watau bita-zaizai, kamar mayakan banzai na kasar Japan wadanda a lokacin yakin duniya ta biyu suke yin harbi kafin su yi tunani.
Idan kuma har ofishin shugaban kasa zai ji shawarata ya tallata siffofin irin mutanen da ake bukata domin zama ministocin da za su maye gurbin wadanda aka sauke, ina ganin abun zai bayar da sha’awa, domin siffofin za su zama kamar haka:Dole mai bukata ya zama mai cikakken biyayya ga shugaban kasa, dole ne ya goyi bayan shirin zaben shekarar 2015, dole ne ya kyamaci sabuwar PDP,duk wanda ya gaisa da dan APC kada ya nemi mukamin, duk wanda surukinsa ko dan hanyan da ke gidansa dan APC ne kada ya nemi mukamin, dole mai bukata ya kasance zai iya kwace shugabancin jam’iyyar PDP a jiharsa tare da taimakon jami’an ‘yan sanda, dole mai bukata ya kasance zai iya fitar da kudi ya jawo magoya bayan gwamnonin sabuwar PDP, kwarewa wajen toshe hanyar da jerin gwanon motocin ‘yan adawa suke bi tare da jifarsu da ledar ruwa dole ne, iya hana jirgin sama mallakar ‘yan adawa tashi da karkatar da jirgin samansu mai saukar ungulu daga sauka a wirin da yake so dole ne. Zama cikin shirin idan an ce kole ya ce cas dole ne.