✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana nuna wa sarauniyar kyan Amurka wariyar launin fata

Misis Nina Dabuluri wadda ta zama sarauniyar kyan Amurka na fuskantar matsalar nuna wariya, saboda asalinta ’yar Indiya ce. Ba itace Ba’Amurkiyyar farko ’yar asalin…

Nina Davuluri, Ba’indiyar Sarauniyar Kyan AmurkaMisis Nina Dabuluri wadda ta zama sarauniyar kyan Amurka na fuskantar matsalar nuna wariya, saboda asalinta ’yar Indiya ce. Ba itace Ba’Amurkiyyar farko ’yar asalin nahiyar Asiya da ta taba samun wannan kambi ba, amma nasarar da ta samu ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin Amurkawa.
A wani taron ’yan jarida da ta kira a rnar Lahadin da ta gabata, ta mayar da martani ga masu takaddama a shafukan sadarwar intanet, wadanda ke nuna takaicinsu kan cewa ’yar asalin Indiya ta ci wannan gasar. Wasu sun yi amfani da sakonnin tweeter, inda suka kirata da sunan Balarabiya ’yar ta’adda.
“Na wuce inda kuke tunani,” a cewar Dubuluri, wadda ta fara shiga gasar Sarauniyar Kyan New York: “A kodayaushe ina ganin kaina a matsayin ’yar Amurka,” injita. Ta ce ta yi farin ciki da ganin cewar wannan gasa da aka farata kusan karni guda, tana da ma’aunin tantance kyau da basira iri-iri.
“Ina cike da farin ciki ganin yadda wadanda suka shirya gasar suka amince da bambance-bamance,” a cewarta. “Ina godiya ganin cewa kananan yara na kallon shirin a gida, wadanda a karshe za su iya kulla alaka da sabuwar sarauniyar Kyan Amurka,” a cewarta.
Lue Brasili, daya daga cikin masu takaddama kan yadda aka yi ’yar asalin Indiya ta ci gasar sarauniyar kyan Amurka, ya koka kan cewa, “kwana hudu da zagayowar ranar da aka kai harin 11 ga Satumba (9/11) aka nadata Misis America.” Shi kuwa Karl Sharro, wani mai korafin kan nasarar Ba’Indiyar Amurkawa, cewa “Alka’ida ce ta juya tunanin wadannan alkalai masu sassaukan ra’ayi.”
Wadanda suka kareta kuwa, mata ne wadanda suka hada da wata Jezebel, inda ta ragagaji ra’ayoyin da ke nuni da wariya, ta ce “ana nuna wariyar ga wannan sarauniyar kyan Amurka ne saboda ita ba farar fata ba ce kawai.
Sarauniya dai za ta kewaya Amurka a shekarar 2014, don tallafa wa rayuwar kananan yara, a matsayinta na jakadiyarsu. Kuma an ba ta tallafin karatu na Dala dubu 50 ta ci gaba da karatunta, inda take da burin zama likita. Nina Dubuluri matashiya ce ’yar shekara 24 da ke karatu a Jami’ar Michigan.