✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ruwan kudi don sake gina cocin Notre-Dame da ya kone

Ana ta samun alkawuran daruruwan miliyoyin Yuro da Fam domin sake gina fitaccen  cocin nan na Notre-Dame bayan da gobara ta lalata wani sashen gininsa.…

Ana ta samun alkawuran daruruwan miliyoyin Yuro da Fam domin sake gina fitaccen  cocin nan na Notre-Dame bayan da gobara ta lalata wani sashen gininsa.

Gobarar wadda aka yi nasarar kashe ta bayan sa’a 15 tana ci, ta kone rufin cocin mai shekara 850.

Amma ’yan kwana-kwanan da suka kashe wutar sun samu hana gobarar kama dakin ajiye kayayayyaki da hasumiyar ginin guda biyu.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labarin ba a san abin da ya jawo gobarar ba.

Lauyan Paris Remy Heitz ya ce ofishinsa na ganin cewa kamar hadari ne ya auku, amma ya ce ya sanya mutum 50 su yi aiki a kan bincike wanda zai kasance mai daukar lokaci kuma mai yawa.

Wadansu na ganin cewa gyarar da ake yi ne a wurin ya haddasa gobara a cocin kamar yadda BBC ya ruwaito.

Abubuwan da suka kone

A tsawon daruruwan shekaru dai ana daukar cocin a matsayin zuciyar bauta ta mabiya Darikar Katolika a kasar Faransa da kuma kasancewa wani wajen bauta da dubban mutane a fadin duniya ke ziyarta a lokuta daban-daban na shekara.

Majami’ar ta kasance wajen da aka killace wasu kayayyakin tarihi masu muhimmancin gaske, da suka hada da wata hular kaya da aka ce Annabi Isa (AS) ya saka da kuma rigar Sarkin Faransa Loius na 9 da aka fi sani da Saint Louis, wanda ya yi zamani sama da shekara 1000 da suka gabata.

Ministan Al’adu na Faransa Franck Riester ya ce “Gobarar ba ta lalata wadannan manyan kayayyakin tarihi masu daraja ba.”

Yanzu mutane sun mayar da hankali ne kan yadda za a sake gina majami’ar.

Tun kafin a gama kashe gobarar, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce za su sake gina cocin.

’Yan kasuwa da masu kudi sun yi alkawarin bayar da kudin da yanzu haka ya haura Yuro miliyan 600.

Taimako na ci gaba da kwarara daga sassan duniya, inda Shugaban Kungiyar Tarayya Turai, Donald Tusk ya nemi kasashen kungiyar su hada kai.

Me ya faru?

An fara ganin wutar ce da karfe 6:43 na safe inda aka yi sauri aka kira ’yan kwana-kwana.

Wutar ta fara cin rufin majami’ar da sauri inda ta kone kayan adon da ke saman ginin.

Mutane sun ji tsoron kada fitacciyar hasumiyar ginin ta lalace.

Wuta kanana a wurare daban-daban sun kama a cikin cocin a cewar Ministan Cikin Gidan Faransa, amma an kashe su kafin su kama wasu wuraren.

A safiyar ranar Talata ce hukumomi suka bayyana cewa an kashe wutar baki dayanta da misalin karfe 10 na kasar.

Mene ne ya lalace?

Masu kula tun safe suka fara aikin duba irin asarar da aka yi a babban birnin kasar.

Bakin dutsen cocin ya bayyana a bainar jama’a a karon farko ga wadanda suka tsaya kallo.

Mai magana da yawun ’yan kwana-kwana ya ce “Gaba daya rufin cocin ya kone, wani sashen rufin ya fado, babu abin da ya rage. Idan da ’yan kwana-kwanan ba su shiga ba da abin ya fi haka lalacewa,” inji a Mista Nunez. Ya kara da cewa, “Ko shakka babu da komai ya ruguje,” kamar yadda jaridar Faransa ta Le Monde ta ruwaito.

Amma wani hoto da aka nuna, ya nuna wata taga wadda wutar ba ta ci ba.

Ana fargabar tagogin gilashi ne wadanda wutar ba ta kama ba.

Ministan Al’adu na Faransa Franck Riester, ya ce an yi sa’a ginin na nan, amma zai iya faduwa.

Mista Nunez ya ce “Gaba daya dai,” ginin na nan da sauransa, amma ya rage karfi, kamar yadda za a iya gani a turakun ginin.

Me zai faru?

Mutane da kamfanoni sun sha alwashin ba da tallafi domin sake gina Majami’ar Notre-Dame.

Kamfanin jirgin sama na Air France ya sha alwashin daukar duk wadanda za su sake ginin zuwa wurin kyauta.

Attajiri Francois-Henri Pinault, Shugaban Kamfanin Kering Group wadanda ke da Gucci da kayan kawa na Ybes Saint Laurent, sun dauki alkawarin ba da Yuro miliyan 100 domin sake gina majami’ar ta Notre-Dame, inji Kamfanin Dillacin Labarai na AFP.

Iyalin Bernard Arnault a madadin kamfaninsu na LBMH sun ba da Yuro miliyan 200.

Kamfanin shafe-shafe na L’Oreal da iyalin da ke mallakin kamfanin na Bettencourt sun yi alkawarin ba da Yuro miliyan 200 domin sake gina majami’ar.

Kamfanin mai na Total, ya yi alkawarin ba da Yuro miliyan 100.

Ita ma Gidauniyar du Patrimoine za ta kaddamar da neman taimako domin sake gina cocin, wanda yana cikin manyan wurare al’ajibi na duniya na  Hukumar UNESCO.

Shugaban Faransa, a jawabinsa ya bayyana gobarar a matsayin kaddara, sannan ya dauki alwashin shiga cikin tsarin sake gina majami’ar. “Za mu sake gina wannan majami’a dukkanmu kuma wannan na cikin kurinmu da aikin da za mu yi a shekaru masu zuwa,” inji  Shugaba Macron a wani jawabi mai tausasawa da ya yi a ranar Litinin.

Shugaban Rasha, Bladmir Putin ya ce zai yi farin cikin tura kwararru domin su taimaka wajen sake gina cocin.

Gwamnatin Ingila ma na duba ta ga da me za ta iya taimakawa kamar yadda Jakadan Ingila a Faransa, Ed Llewellyn ya bayyana.

Ministan Al’adu na kasar Spain Jose Guirao ya ce kasarsa na dubi a kan yadda za ta iya taimakawa.

“Amma a yanzu babban abin yi shi ne jajanta musu da ba su kwarin gwiwa da abin da suke so,”  inji shi.

 

Kaddarorin da ke cikin majami’ar

Masu ba da agajin gaggawa sun yi nasarar cire muhimman abubuwa na addini daga wurin, har da “Kambin (hular) kaya da Annabi Isa  (AS) ya sanya kafin gicciye shi,” inji su.

Rigar da Sarki Louis ID ya sanya lokacin da ya kawo kambin kayar da Annabi Isa (AS) ya sanya ita ma an dauke ta.

Masanin tarihi, Camille Pascal ya sanar da gidan jaridar BFMTB cewa “Tarihi marar misaltuwa ne,” ya lalace sanadiyyar gobarar.

“Abubuwan dadi da na rashin dadi duka an sanar da su ta karaurawar majami’ar Notre-Dame. Muna bakin ciki da abin da ya faru,” inji shi.