Da Dumi Dumi

Ana takun-saka tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un

Rundunar Sojin Koriya ta Kudu ta bayyana cewa Koriya ta Arewa ta harba wasu makamai masu linzami biyu da ke cin gajeren zango, inda take zargin ta harbo su ne daga gabar tekun kasar ta Gabas.

Wannan ne karo na biyu da kasar ke harba irin wadannan makamai cikin ’yan kwanakin nan inda ta harba wasu makaman biyu a cikin Tekun Japan a makon jiya.

Ministan Tsaron Koriya ta Kudu, Jeong Kyeong-doo ya bayyana cewa wadannan makaman da Koriya ta Arewa ta harba a wannan karo, sun sha bambam da wadanda ta harba a makon jiya.

Ya ce makamai masu linzami da kasar ta harba da ke cin gajeren zango sun nufi Arewa maso Gabas inda suka shafe tafiyar kusan kilomita 250 kafin su sauka a cikin Tekun Japan.

Koriya ta Arewa, ta bayyana makaman da ta harba a makon jiya a matsayin gwaji kuma a matsayin gargadi ga Koriya ta Kudu ganin cewa Koriya ta Kudun na shirin wani atisayen hadin gwiwa da Amurka a watan gobe.

ADVERTISEMENT

Sai dai Amurka ta yi watsi da wannan gwajin da Koriya ta Arewa ta ce ta yi, inda Shugaba Trump na Amurka ya ce, kasashe da dama suna gwajin makamai masu linzami da ke cin gajeren zango.

Kuma rahotanni sun ce Mista Trump ya aika wa Shugaban Koriya ta Arewa Kim-Jong-un hotunansu a ganawar da suka yi a iyakar Koriya biyu a watan Yuni.

Wani jami’in Fadar Gwamnatin Amurka ya bayyana cewa yana sa ran nan da ’yan kwanaki kadan za a fara wata tattaunawa a tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Share