✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da Alaramma Ahmad Suleiman

Iyalai da ’yan uwan Alaramma Ahmad Sulaiman da yanzu  yake tsare a hannun mutanen da suka yi garkuwa da shi, sun ce suna nan suna…

Iyalai da ’yan uwan Alaramma Ahmad Sulaiman da yanzu  yake tsare a hannun mutanen da suka yi garkuwa da shi, sun ce suna nan suna tattaunawa da masu garkuwa da shi don ganin malamin ya samu ’yancin kansa.

Malam Muhammad Kabir, wanda ya yi magana a madadin iyalan malamin ya ce ba zai  bayyana adadin kudin da masu garkuwa da malamin suke nema ba sai dai a cewarsa ana samun ci gaba a tattaunawar.

“Ina tabbatar wa al’umma cewa Malam yana nan cikin koshin lafiya kuma insha Allahu nan ba da dadewa ba zai samu ’yanci daga hannun masu garkuwa da shi din,” inji shi.

Ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su yi wa malamin addu’a, kasancewar babu wani tsanani da addu’a ba ta maganinsa.

Shi dai Malam Ahmad Sulaiman, wadansu mutane ne suka yi garkuwa da shi ne a ranar Alhamis ta makon jiya  a kan hanyar Sheme da Kankara da ke Jihar Katsina, lokacin da yake dawowa daga Jihar Kebbi tare da wadansu mutum biyar, inda aka ce sun nemi a biya Naira miliyan 300 a matsayin kudin fansa.