Da Dumi Dumi

Ana tuhumar alkalan wasa da yin coge a Singafo

Wasu alkalan wasa su uku ’yan asalin kasar Lebanon sun shiga komar alkali a wata kotu da ke Singafo bayan ikirarin da suka yi cewa an ba su toshiyar baki don yin coge a wani wasa da suka yi alkalanci a kasar  a karshen makon jiya.
Alkalin ya ce ya yanke wa mataimakin alkalin wasa mai suna Ali Eid, dan kimanin shekara 33 da kuma Abdallah Taleh mai kimanin shekara 37 hukuncin daurin wata uku a gidan kaso kowannensu bisa zargin sun hada kai da wani attajiri mai suna Eric Ding Si Yang, wajen aika musu da wasu karuwai suka yi lalata da su don ba kulob dinsa damar samun nasara a wasan.
Shi kuwa alkalin wasan mai suna Ali Sabbaagh kotu ta dage sauraron kararsa ce har sai bayan ta gudanar da cikakken bincike kafin ta yanke masa hukunci. Alkalin kotun ya kara da cewa “saboda laifin da ka aikata na shawo kan abokan aikinka wajen karbar toshiyar baki ta yin lalata da karuwai da wani attajiri ya gabatar muku don yin magudi kulob dinsa ya samu nasara ta sa ban yanke shawarar hukuncin da zan yi maka ba a halin yanzu kuma akwai yiwuwar ka shafe lokaci mai tsawo a gidan yari don kai ne kanwa uwar gami”.
Jim kadan bayan alkali Low Wee Ping ya yanke hukunci ne sai mataimakan alkalan wasan biyu da aka yanke wa hukuncin suka barke da kuka kuma suka yi godiya ga Allah bayan da alkalin ya shaida musu cewa maiyiwuwa a rage m kwanakin da za su yi a gidan kaso bisa juyayi da kuma nadamar da suka yi.
Haka kuma tuni kotun ta tuhumi attajiri Eric Ding Si Yang da laifin daukar nauyin samar da karuwan da aka yi amfani da su don janyo hankalin alkalan wasan su yi magudi a wasa tsakanin kulob din Tampines da ke Singafo da kuma na India’s East Bengal.
Ta ce abin da attajirin ya aikata kotu ta dauke shi ne a matsayin bayar da cin hanci da karbar rashawa da hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.