Search
Subscribe
Ana tuhumar Okocha da laifin mallakar kudin haramun

Ana tuhumar Okocha da laifin mallakar kudin haramun

Tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Austin Jay-Jay Okocha yana fuskantar tuhuma a wata kotu da ke Abderdeen a kasar Sukotland saboda zargin mallakar kudi ba bisa ka’ida ba, da hakan ya saba wa dokar kasar.

Jaridar Thesocttishsun ta ruwaito tsohon kyaftin din  kotun ta tuhume shi ne a wani zama da ta yi a makon jiya sai dai bai amsa laifinsa ba.  Daga nan ne kotun ta bayar da belinsa.  Sai dai kotun ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci da ba ta sanar ba.

Dan kimanin shekara 45 Okocha dai yana fuskantar laifuffuka biyu ne a Sukotland da suka hada da mallakar kadarori ba bisa ka’ida ba da kuma yin bad-da kama ko yin coge ko hada baki da wasu wajen yin kasuwanci ta barauniyar hanya a cikin kasar ba tare da sanin hukuma ba.

Jami’an ’yan sanda sun ce tun a shekarar 2015 Okocha tare da wasu mutum biyar mazauna kasar suka aikata laifukan sai dai a yanzu ne da dan kwallon ya ziyarci kasar a makon jiya suka yi ram da shi kuma suka tasa keyarsa zuwa kotu don fara sauraron karar.

Akwai yiwuwar a yanke masa tare da sauran abokansa hukunci idan aka same su da laifi, kamar yadda rahoton da ’yan sandan kasar suka fitar.

Okocha dai ya yi kwallo a kasashe da dama da suka hada da Ingila da Turkiyya da sauransu.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin