Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ana yi ka tsaro riqon sakainar kashi a Areka

Ana yi ka tsaro riqon sakainar kashi a Areka

Ana yi wa tsaro rikon sakainar kashi a Arewa

Assalam Edita. Ka mika sakona zuwa ga Shugaba Buhari kan yadda ake yi wa tsaro rikon sakainar kashi musamman a  Arewa. Mu fa mun yarda da kai, yarda ce ta sa muka zabe ka har muka hakikance cewa, saboda a magance matsalar Boko Haram to ga shi an shiga sabuwar gwamnati, amma komai sai kara lalacewa yake yi. Don Allah Baba Buhari ka gyara, yanzu kauyukan Katsina da Zamfara babu damar zuwa gona.

Daga Yakubu Abdullahi Fulatan,  Rogo, Jihar Kano 07035224185.

Mu yi koyi da Bashir Umar

Assalam Edita da fatan kana lafiya amin. Don Allah ina so ka mika min sakon jinjinata ga sojan saman nan Bashir Umar, bisa gaskiya da dattakon da ya nuna na tsintar kudin da ya kai Yuro 37.000 a filin jirgin saman Kano ya mayar wa mai shi. A gaskiya ya nuna hali mai kyau.

Daga 08032436477.

Nadin sababbin ministocin Buhari

Baba Buhari, ministocinka ka ba wa malaman addini saboda rikon amana da gaskiyarsu. Sannan jaridar Aminiya don Allah, mahukunta su yi doka a kan bankuna idan mutum yana son karbar kudi a kanta a ba shi idan yana so a ATM ya cire.

Daga Ahmed Gombe 08135284541.

Damina: A kula da tsabtace magudanun ruwa

A daidai lokacin da damina ke dada zurfi a wasu jihohin Arewa, muna kira ga jama’a su kula da tsabtace magudanun ruwansu da kuma kauce wa yin gine-gine a kan hanyar ruwa gudun haduwa da ambaliya. Da fatar Allah Ya ba mu damina mai albarka.

Daga Muddassir Muhammad Tafawa Balewa, 08131534652.

Ta’aziyya ga jama’ar Borno

Amincin Allah ya tabbata a gare ku Aminiya. Muna jajanta wa al’ummar Jihar Borno, da na Najeriya baki daya sakamakon mummunan harin da ’yan bindiga marasa imani  suka kai a kan masu jana’iza a jihar. Abin bakin ciki ne da jimami ganin yadda suka janyo asarar mutuwar mutane da dama wadansu kuma suka jikkata. Muna fata Allah Ya kiyaye aukuwar haka nan gaba kuma Ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a Najeriya da duniya baki daya amin don darajar fiyeyen hallitta Annabi Muhammad (SAW).

Daga Alhaji Umar Foreber Gashuwa, 08108003333.

Mun amince da sulhu da ’yan bindiga a Zamfara

Tabbas mu al’ummar Jihar Zamfara, mun ga tsarin da ka yi a lokacin mulkinka wajen sulhu da ’yan bindiga. Don haka mun gamsu da wannan gwamnati, kuma mun yi na’am da tsarin don kawo karshen matsalar tsaro a  Zamfara.

Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu, Gusau. 08069807496

Kira ga Shugaba Buhari

Assalamu alaikum Edita. Don Allah a ba mu dama mu yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Bahari kan fitar da sunayen ministocinsa na wannan karo. Hakika mu matasa an bar mu a baya wajen ganin an sanya mu cikin tafiyar duk da irin gagarumar gudunmawa da muka bayar wajen ganin an kafa wannan gwamnatin ta APC. Don haka ina kira ga Shugaban Kasa ya sanya matasa cikin tafiyarsa domin su ma su ba da tasu gudunmawar. Da fata wannan kira namu zai kai ga inda ya dace.

Daga Sani Mohammed Chindo, da Alhaji Brah Dada Kukuri Potiskum 08030918913/08060775533.

Tunatarwa ga Gwamnatin Katsina

Salam. Don Allah Edita, ku mika mana tunatarwarmu ga Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Dan Majalisar Dokokin Jihar daga yankinmu cewa su yi wa Allah da Manzonsa su duba annobar zaizayar kasa da ke neman cinye garin Mazoji Matazu. Da fata sakonmu zai kai ga kunnen da ya kamata.

Daga Umar A. Umar Mazoji,  07054286772.

Gargadi ga masu zanga-zangar Sudan

Gwamnatin rikon kwarya  ta Sudan ta yi da-na-sanin abin  da sojoji suka yi a kan masu zanga-zanga kwanakin baya. Har an kama wadansu daga cikin sojojin. Amma akwai ranar Lahira, tabbas Allah zai yi hukunci na gaskiya.

Daga I. Y.Baba Dt Kano 07014762738. 

Muna murna da dawo da ‘Dausayin Kauna’

Assalamu alaikum Edita. Barka da kokari a gaskiya mun ji dadi matuka da aka dawo mana da shafin ‘Dausayin Kauna.’ Sannan ina mika gaisuwata ga ilahirin masoya wannan shafi mai albarka maza da mata.

Daga Abdullahi Lawali Abul Aiman Gusau. 07037001720.

Tsokaci game da zaben Kano

Assalam Edita. A Kano an yarda da shi amma na Zamfara an soke, to, akwai lauje a cikin nadi. Kuma APC ta sani matukar Kano ta koma hannun PDP to ina tabbatar muku cewa, mutuwar APC ta zo ke nan. Domin a Kano, za a dawo da filin lalata kati kuma duk wanda ba dan PDP Kwankwasiyya ba ya shiga uku, in kunne ya ji…

Daga Dahiru Kano 08035856904.

A gaggauta kammala gyaran hanya

Kira ga Gwamnatin Tarayya don Allah a taimaki masu bin hanyar Kano zuwa Zariya da Kaduna zuwa Abuja, mutane suna ta mutuwa a sanadiyyar aikin hanyar. Wani wurin kamar ba za a yi ba, don Allah a gaggauta a gama aikin nan. Allah Ka taimake mu Ka taimaki Muhammadu Buhari. Allah Ya kawo mana karshen kashe-kashen da ake yi wa bayin Allah wadanda ba su san  hawa ba ba su san sauka ba.

Daga Usman 440 Bayan Nepa Malumfashi Kt 08135815119.

Kowa zai iya bayyana ra’ayinsa

Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga ’yan uwa masu kiran wayar mutane suna zagi da kalamai na batanci saboda mutum ya bayyana ra’ayinsa a wannan shafi. Ya kamata ’yan uwa su gane wannan filin ra’ayi ne kai ma ka fadi naka ra’ayin ba zagi ba.

Naku Angon Asmi Abban Ammar da Suhailat Auwal Yunusa Sauna 08107737474

Almajiranci da bara ba alheri ba ne

Kira ga gwamnati don Allah ku yi nazari kafin ku hana almajiranci da bara, saboda addinin Musulunci ma ya hana bara. To yana da kyau a je a nemi ilimin addinin Musuluci.

Daga Is’haka Maidawa Yelwan Shendam Jihar Filato 08064558922.

Kira ga Babban Jojin Najeriya

Salam Edita. Da fatar kana lafiya ina so in yi amfani da wannan dama in yi kira ga Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Tanko Muhammad game da sakamakon zaben Jihar Kano. Kowa ya san ba a yi wa Kano adalci ba domin wanda suka zaba ba shi aka ba su ba kuma an ce mu yi cancanta, amma saboda ba dan APC ne ya ci ba shi ya sa aka hana shi. To mu dai yanzu muna gode wa Allah da shari’ar ta dawo hannunku domin mun san ku al’umma kuke yi wa aiki da kamanta gaskiya ba wai jam’iyya ba, kuma idan an ce shaida ce, to akwai ’yan jarida da jakadun Amurka da suka sa ido su ma shaidu ne. Daga karshe ina yi muku addu’a Allah Ya ba ku ikon kamanta gaskiya.

Daga Nasiru Kano, 09069985179.

Sharar Asabar: Jinjina ga Gwamnan Legas

Assalam Edita. Don Allah ka mika min gaisuwata ga sabon Gwamnan Jihar Legas game da sharar Asabar din duk karshen wata. Za mu kara ba wa gwamnatin Legas cikakken hadin kai game da wannan tsari mai amfani.

Daga Maikudi Zeze dan Okada Hausa Layi Ajegunle Apapa Legas, 09025253393.

 

Ta’aziyya ga jama’ar Sakkwato

Ya Allah Ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon aika-aikan ’yan bindiga a Jihar Sakkwato da Jamhuriyyar Nijar. Allah Ka kiyaye aukuwar hakan nan gaba ka kuma kiyaye mu da sharrin ’yan bindiga a duk fadin duniya. Wadanda ya shafe su Allah Ka ba su sauki amin.

Daga Danmanya da Abu Yazyd Loko 08059742509.

Kira ga Gwamnan Jihar Kebbi 

Assalam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnanmu Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, game da tallafin noman rani da ake bayarwa. Shin mu manoman damina me ya sa aka manta da mu, ko don ba mu da Fadama? Don Allah Gwamna a duba.

Daga Yahaya Abdullahi Yamama Argungu Jihar Kebbi 08143546257.

Ina jinjina ga Ummul Kaltume

Ina jinjina wa Ummul Kaltume bisa tsayawarta ta ceto mutum 10 daga hannun ’yan Boko Haram, aikin da maza suka kasa yi. Allah Ya yi miki jagora amin.

Daga Shehu Sahabi Wurno No 16 Dallatu Road, Sakkwato 08065901299.

Martani kan muhawarar filin Dausayin Kauna

Assalam na ji duk muhawarar da aka yi a filin ‘Dausayin  Kauna.’ Maganar gaskiya mata sun fi rikon alkawari, in ka ga mace ta saba alkawari ga namiji to dama son bai je zuci ba, amma in dai ta amsa har zuci to duk runtsi tana tare da kai. Amma mu maza muna sabawa. Za ka ga namiji ya samu lalura ya yi kashi da fitsari a kwance, ta gyara tana tare da shi. A haka sai ka ga ta haihu, in shi ne ba zai rabe ta ba. Sai ka ji ya ce a kai ta gidansu, saboda jinyar mace sai mace. Don haka gaskiya mata sun fi maza rike alkawari.

Daga  Alhaji Husaini Tsoho Imawa Kura, 08165610365.

Gwamnan Adamawa ka ci ka alkawari da ka yi

Salam Edita, don Allah ku mika min sakona zuwa ga mai girma Gwamnan Jihar Adamawa Amadu Fintiri, da ya cika mana alkawarin da ya yi mana a lokacin yake yakin neman zabe! Ka tayar mana da Company (PW) NG. Limited. Da ke Binkola a Karamar Hukumar Mayo Belwa, a jihar Adamawa wanda tsohon Gwamnan jihar wato Murtala Nyako ya kawo mana don ci gaban jihar mu ta Adamawa wanda tsohon Gwamnan Bindow ya rufe. Nagode Allah ya saka muku da alheri.

Daga Faisal Usman Binkola, Mayo Belwa jihar Adamawa, 08039258288:

Matsalar taro: ’Yan Najeriya mu taimaka wa Gwamnati

Salam Edita, ina kira ga ‘yan Najeriya musamman ‘yan Arewa dangane da barazanar ta’addanci da ke fuskatan wasu yankuna na Arewa, da cewa a fito karara a taimakawa gwamnati wajen kawar da wadannan miyagun ayyuka da wasun mu suke aikatawa da sunan ramuwa ko kuma daukan fansa, idan ba haka ba komai namu zai tabarbare babu wanda zai so ya hada wata kyakkyawan mu’amala damu, za a guje mu a kuma guji yankin mu daga karshe mu koma baya a duk wani harkar ci gaba a barmu muna fada da junanmu da haddasa mummunan gaba a tsakaninmu. Don haka in har muna son yankinmu da kasarmu to sai mun taimakawa gwamnati wajen zakulo bata gari da ke cikin mu, ba tare da shakku ko tsoro ba sai don kawai tabbatuwar samar da zaman lafiya da wanzuwar arziki a yankin mu da kasarmu baki daya. Allah ya daukaki yankin Arewa da kasarmu Najeriya baki daya.

Daga Basiru Danbazazzagi 08058591624, 08130616265.

Shawara ga Musulmi da Kirista

Salam Edita, shawara ga Musulmi da Kirista na Najeria, yakamata su rinka zabar shugabanni masu ilimin addinansu domin duk wanda ya fahimci addininsa da kyau, ba zai kauda kai a halin da jama’ar kasa ke ciki ba.

Daga Abdurahman Mai Agogo Hadejia, 08033836968.

Matakin kafa Ruga zai magance rikici

Salam dan Allah Edita, ka ba ni dama na tofa albarkacin bakina dangane da yunkurin da Gwamnatin Tarayya ta yi nasamawa Fulani matsugunni guri daya tak. Hakika ni a ganina wannan mataki ya yi daidai domin ta haka ne za a magance rikicin manoma da makiyaya a kasar mu Najeriya.

Daga Bala Laba mai Barcelona Garado Itas/Gadau jihar Bauchi, 08088001511.

Kira ga iyaye akan ilimin ‘ya’ya mata

Editan AMINIYA, ina kira ga iyaye da su bai wa Gwamnati hadin kai game da sanya yara mata makarantun firamare domin samun cikakken ilmin zamani.

Daga Saminu Mayentea Ung Alkali Batsari. 08036773485.

Kira ga Buhari

Assalam Edita, ka ba ni dama in yi kira ga shugaba Buhari ya aiwatar da shirin tsugunar da Fulani makiyaya za a sami lafiya cikin kasa. Daga Umar.A Umar Airport Abuja 08187592568

Tsaron a Zamfara: Kira Ga Shugaba Buhari         

Salam Editan AMINIYA mai farin jini. Don Allah ka bani dama in yi kira ga shugaba Buhari da ya yi wa Allah da Annabi ya dauki matakin gaggawa ga jihar Zamfara kamar yadda ya yi wa na Boko Haram da ya canza sojojin da ya turo tare da Kwamandojinsu kuma kada a ajesu a cikin gari a kaisu daji. Kuma a yi haka bada bata lokaci ba. Kauyukan Zamfara suna cikin mawuyacin hali na hasarar rayuka. Kuma ina yabawa Gwamna Matawalle domin yana iya kacin kokarinsa, amma Shugaba Buhari ya kara taimakawa.

Daga Umar A. Moh’d. Gusau (MAMU NAMU) 08081167862

Kashe yaron alkali don Allah a yi adalci

Salam Edita, na kadu da labarin kashe yaro da matar alkali tayi a jihar Gombe. Ina roko don Allah Gwamnan jihar Gombe da mataimakansa su tabbata an yi adalci a wannan batun. Kar aga wai matar alkali ce ayi watsi da maganar. Don Allah abi ma wadanna bayin Allah hakkinsu. Daga Abdullahi Zauro Jihar Kebbi, 080690773631.

Kira ga Buhari da Gwamnan Katsina

Assalamu alaikum, don Allah ina so in yi kira ga mai girma shugaban kasa da kuma Gwamnan Katsina su taimaka mana a bude mana makarantar ‘School Of Medicine’ a Katsina ko don ci gaban al’ummar jahar mu da kasa baki daya. Allah Ya sa a dace Amin. Daga Fatima Katsina 080 34579529.

Ga Gwamnati

Edita, don Allah ba ni fili in yi magana kan tsaro. Rashin tsaro ya samu ne dalilin talauci da rashin ilimi wanda ya haifar da gurbacewar tarbiyya har ya kawo fashi da makami, satar mutane da sauran miyagun aiki. Gwamnati na kokari sosai wajen gyara al’umma amma ya dace a yi doka dole iyaye su ba ‘ya’yansu tarbiyya a tanaji hukunci mai tsanani ga wanda ya ki yi, aba matasa aiki, a koya masu sana’a, a basu ilimi da jari kyauta, a cusa masu tsoron Allah da kaunar kasa, a kara daukar matakan dakile safarar miyagun kwayoyi sannan a kara gina gidajen yari.

Daga AmiRu Isah Bakori 08084213547.

Kira ga ’Yan Najeriya

Salam Edita, ina kira ga ’yan Najeriya da mu yi wa shugaba Buhari uzuri ga sha’anin gwamnati da zarar ya ce zai yi abu sai mu damu mu sani Allah kadai ke cewa zai yi abu ya yi shi lokaci daya, shi dan adam ne kamar kowa.

Daga Sufiyanu Aliyu Maishago Dakkwa Abuja 08161788025.

Taya murna ga iyalan Magajin Garin Daura

Assalamu alaikum Edita, ina taya iyalai da al’ummar garin Daura murnar kubutar da mai girma Magajin Garin Daura Allah Ya kiyaye al’ummar musulmi baki daya. Daga 08033359947.