Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ana yunkurin juyin mulki a Benezuela

Shugaban Venezuela Nicolas Maduru
Shugaban Venezuela Nicolas Maduru

Shugaban ’yan adawa da Amurka ke goyon baya a matsayin shugaban wucin gadi na kasar Benezuela Juan Guaido ya ce, “babu ja da baya” a yunkurinsa na kawar da Shugaban Kasa Nicolas Maduro.

Dubban masu zanga-zanga ne suka fita kan tituna a Babban Birnin Kasar, sai dai sojoji masu goyon bayan Maduro sun tarwatsa su da harbin bindiga da kuma watsa musu ruwan zafi.

ADVERTISEMENT

Wani faifan bidiyo da aka nuna ta gidan talabijin ya nuna yadda wata babbar motar sojoji ke bin masu zanga-zangar, wadanda ke jifansu da duwatsu. Gwamnati ta ce harbin bindiga ya samu daya daga cikin sojojinta.

A nan birnin Washington kuma, Shugaban Kasa Donald Trump ya fadi ta shafin Tiwita cewa, yana lura da dukkan abin da ke faruwa, inda ya kara da cewa, “Amurka tana tare da mutanen Benezuela da kuma ’yancinsu.”

ADVERTISEMENT