✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zabe lafiya a Kaduna

Mutanen Jihar Kaduna sun fito domin kada kur’arsu kamar yadda doka ta tanada musu. Wakilinmu da zagaya, ya gane wa idonsa yadda mutane suka fito…

Mutanen Jihar Kaduna sun fito domin kada kur’arsu kamar yadda doka ta tanada musu.

Wakilinmu da zagaya, ya gane wa idonsa yadda mutane suka fito suka tsaya a kan layi ba tare da rikici.

Wani wakilin Jam’iyyar APC a Unguwar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar ta Arewa, Injiniya Rabi’u Ibrahim wanda aka fi sani da Rabe mai gaya ya bayyana mana cewa zabe yana lafiya daidai.

Hakanan kuma wakilinmu ya rawaito mana cewa an zuba jami’an tsaro sosai domin hana tayar da hankali.