✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zaman zullumi a Jos saboda #EndSARS

Matasan Kiristoci da takwarorinsu Musulmi na tayar da jijiyoyin wuya kan rufe hanya

Mazauna garin Jos na Jihar Filato sun shiga cikin zullumi bayan masu zanga-zangar #EndSARS sun tare babbar hanyar shiga kwaryar garin.

Fargaba ta tilasta wa ‘yan kasuwa a Kasuwar Terminus da ke daura da babban titin Ahmadu Bello rufe shagunansu domin guje wa abin da ka je ya dawo.

Tun da misalin karfe 10:15 na safiyar Talata matasa Kiristoci suka tare hanyar suna wake-waken #EndSARS; a daya hannun kuma takwarorinsu Musulmi na kalubalantar rufe hanyar.

Wakilinmu ya tabbatar da jin karar harbe-harbe a yankin inda aka ga matasan ke dauke da adduna.

Yanayin ya tilasta wa mazauna guduwa daga wurin da ake tayar da jijiyoyin wuyan.

Zuwa lokacin da wakilinmu ya aiko wannan rahoto jami’an tsaro ba su kai ga isa wurin ba.