✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin almajirai da rataye dan shekara tara

Al’ummar Unguwar Kuntau a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano sun shiga alhinin rasuwar wani karamin yaro mai suna Najib Kamal mai shekara tara, wanda…

Al’ummar Unguwar Kuntau a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano sun shiga alhinin rasuwar wani karamin yaro mai suna Najib Kamal mai shekara tara, wanda aka tashi aka ga gawarsa rataye a cikin gidansu. Hakan ya sa al’ummar unguwar suka shiga rudani tare da tambayoyin kan wa ya kashe yaron da kuma a kan wane dalili aka kashe shi?

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis din makon jiya da misalin karfe 3:00 na rana inda aka ga gawar yaron rataye a jikin igiya da aka daura a jikin wata kofa da ke cikin gidansu.

Rahotanni sun ce lokacin da lamarin ya faru babu kowa a gidan sai mahaifiyar marigayin da kanensa Nabil sai kuma almajirin gidansu mai suna Sani Musa.

Malama Na’ima Rabi’u  mahaifiyar marigayin ta bayyana wa Aminiya cewa lokacin da lamarin ya faru tana bene ba ta san abin da ke faruwa ba, sai yamma likis lokacin da ta nemi danta ne aka dauko gawarsa aka kawo mata. “Ina sama a kwance da yamma  sai na ce da wata yarinya ta je ta kirawo min shi da kanensa a kofar gida. A zatona suna can suna wasa. Da ta sauka kasa sai ga ta ta kawo min gawar Najib. A nan ne muke tambayar Nabil yadda aka yi sai ya ce lokacin da ya sauka kasa sai ya ga Najib a rataye a jikin wata igiya da aka daura a jikin kofar yana barci don haka sai ya kira almajirin da yake yi musu wanki a waje mai suna Maharazu don ya kwance yayan nasa. Shi kuma da ya zo sai ya kwance shi ya dauko shi ya shimfida shi a dakin kasa. Bayan haka kuma ya hawo sama wurina ya karbi abincinsa ya zauna a kasa ya ci ya yi tafiyarsa ba tare da ya sanar da ni halin da ake ciki ba.” inji ta.

Game da mutanen da suke cikn gidan lokacin da lamarin ya faru, Malama Na’ima ta ce, “A lokacin daga ni sai shi marigayin da kanensa wanda muke tare da su a kasa sai kuma wani almajirin da nake aikensa mai suna Sani. Shi almajiri Sani kwanansa uku bai zo gidan ba, sai a ranar ya zo karbar abinci. Kasancewar ba yau ba yake min wani irin halaye idan na aike shi ba ya zuwa ko kuma idan ya je aike ya dawo sai dai kawai ya ajiye ya yi tafiyarsa ba zai yi min magana ba.Wannan ya sa na yi masa fada a kan hakan. Shi ke nan sai ya daina zuwa gidan sai a ranar da lamarin zai faru sai ga shi ya zo, ni kuma na ce ba zan ba shi abinci ba. Ni da na gama abin da nake yi a kasa sai na hau bene na bar yaran a kasa suna wasa. Ashe  wannan almajiri Sani ya dawo cikin gidan ya zauna ban sani ba.”

Malam Kamal Aminu Baba mahaifin Najib ya shaida wa Aminiya cewa likitoci sun tabbatar da cewa Najib ya rasu ne ta hanyar ratayewa. “Lokacin da muka isa asibiti likitoci sun tabbatar min cewa ya mutu ne ta hanyar ratayewa.”

Malam Kamal ya ce, “Kana ganin daurin igiyar ka san ba yaro ne ya yi ba, saboda an daura ta ce a saman kofa wanda ko ni ta wuce tsayina. Wannan yana nuna cewa daukar yaron aka yi aka sa wuyansa a cikin kullin igiyar ba wai shi da kansa ya aikata haka ba. Haka kuma kullin da aka yi wa igiyar zarge ce yadda idan wuyan mutum ya shiga zai tamke shi.”

Ya ce almajiri Maharazu ya tabbatar masa cewa ya samu gawar marigayin a rataye ne inda shi da kansa ya sauke ta. “Lokacin da kanen marigayin ya shaida mana abin da ya faru mun tambayi almajiri Mahrazu inda ya tabbatar cewa ya samu Najib a rataye shi ne ma ya kwanto shi da hannunsa. Sai dai bai sanar da mahaifiyar Najib din ba.  Haka kuma ya shaida mana cewa lokacin da zai shigo gidan ya ga Sani a kofar gidan.”

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta DSP Abdullahi Haruna ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ta fara bincike a kan lamarin, “Ana zargin wadansu almajirai biyu wato Maharazu Yusuf da Sani Musa wadanda suke gudanar da aiki a gidan su marigayin da rataye yaron. Yanzu haka jami’anmu sun fara bincike a kan lamarin don gano hakikanin gaskiya,” inji shi.