✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin amarya da kisan angonta

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wata amarya a unguwar Yakasai cikin jihar, bisa zargin ta da kisan angonta ta hanyar sanya masa…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wata amarya a unguwar Yakasai cikin jihar, bisa zargin ta da kisan angonta ta hanyar sanya masa guba a cikin abinci, bayan kwana 12 da aurensu.

Aminiya ta rawaito cewa bayan da angon mai suna Umar Sani ya ci abincin amaryar tasa ne ya fara korafin ciwon ciki, inda aka garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda ya ce ga garinku nan.

Binciken Aminiya ya gano cewa  akwai dangantaka ta jini  tsakanin amarya da angon, wanda iyayensu suka hada auren zumunci sai dai an ce amaryar dama tun da farko ta nuna rashin amincewarta ga auren, lamarin da iyayenta suka yi watsi da shi; inda suka ci gaba da shirye-shirye, tare da gudanar  da auren.

Abdullahi Sani dan uwa ne ga marigayi Umar. Ya bayyana cewa sun zargi amaryar ne kasancewar tun farkon auren ba ta son angon nata, “ba wai rashin son angon nata ne kawai dalilinmu na zarginta ba, mun sami bayanai cewa kafin ta aiwatar da mugun nufin nata ta rika tambayar ’yan uwanmu game da gubar da take saurin kisa. Haka kuma yaron da ta aika ya sayo mata gubar, ya bayar da shaida a kan hakan.”

Aminiya ta tattaunan da yaron da wacce ake zargin ta aika ya sayo mata gubar, wanda aka boye sunansa saboda shekarunsa, ya bayyana cewa a ranar Alhamis din makon da ya gabata ce amarya Sadiya ta aike shi ya sayo mata guba, inda ya sayo ya ba ta, sai dai a cewarsa ba ta gaya masa abi da za ta yi da ita ba. 

DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa ’yan uwan marigayin ne da suka hada da Saminu Salisu da Abdullahi Garba suka sanar da ofishin ’yan sanda na k/Wambai game da lamarin, inda ’yan sanda suka je unguwar Yakasai don kama amaryar amma sai suka tarar ta gudu. Don haka da suka je gidan iyayenta, inda a karshe aka kama ta.

Ya bayyaan cewa a yanzu haka wacce ake zargin tana hannunsu,  da zarar bincikensu ya kammala za a gurfanar da ita gaban shari’a.