Da Dumi Dumi

Ana zargin bako da sace yaro a Ebonyi

Iyayen yaron da aka sace, Silas Onyeko da matarsa
Iyayen yaron da aka sace, Silas Onyeko da matarsa

Hankali ya tashi a Unguwar Ogbe Hausa da ke Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi bayan da aka zargi wani mai suna Okechukwu da ya je bakunta gidan iyalan wani mutum mai suna Silas Oyoke, kuma bayan ya gama sada zumuncin da ya kawo shi daga garin Fatakwal a Jihar Ribas, inda yake harkokin kasuwancinsa, sai ba a ga wani dan mai masaukin nasa mai suna Esomchi ba. Majiyarmu ta ce tun daga nan ne shakku da zargi suka shiga ran Silas Oyoke game da bakon nasu, ganin bakon ya tafi an neme shi kasa ko sama an rasa.

Wanda ake zargi da sace yaron da ba a san ko ina ya nufa da shi ba, wakilin Aminiya ya samu labarin cewa dan asalin Karamar Hukumar Ezza ta Arewa ne mazaunin Fatakwal.

A cewar majiyar tun farko bakon ya so iyayen yaron su ba shi wannan yaro su tafi wurin harkokin kasuwancinsa ne amma suka ki, sai ya roki iyayen Esomchi, su ba shi wurin kwana in ya so da safe ya wuce.

Mahaifin jaririn ya ce, “Tun cikin watan Satumban da ya wuce ne wani mutum ya zo ya roke ni Omyo, na yi masa alfarma. Ya ce, in raka shi kasuwa zai sayi garin kwaki buhuna da yawa ni kuma na raka shi kasuwar kwakin da ke Layin Gunning. Bayan na dawo gida can da yamma sai na ga bakon ya dawo gidana na ce kai kuma me ya dawo da kai gidan nan bayan na raka ka kasuwa? Sai ya ce, da ni ba ya son ya bi motar kaya ce, yana so ya kwana a nan da safe ya wuce.  Tun daga wannan lokaci ne matata ba ta ga yaron ba, ta sanar da makwabta.”

Ya ci gaba da cewa, “Ashe cikin ’ya’yana wata yarinya ta ga lokacin da suka fita da yaron ya ce za su je ya saya masa biskit tun daga nan na fara kiran layin wayar da ya ba ni, na yi ta kiran layinsa ya ki daga wayar har tsawon sa’o’i biyar wayar na kara, amma bai amsa kirana ba haka muka bazama nema ko Allah zai sanya mu dace ba mu gan shi ba.”

ADVERTISEMENT

Wakilin mu ya tuntubi karamin ofishin ’yan sandan Ekeaba, inda suka tabbatar da faruwar haka, sai dai jami’in da aka tuntuba ya ce sakacin mahaifan yaron ne ya jawo haka.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya