✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin coronavirus ta kashe likita a Akwa Ibom

Ana zargin cutar coronavirus ce ta kashe wani likita mai suna Dakta Dominic Essien, kuma malami a tsangayar Tsarin jiki da ke jami’ar Uyo babban…

Ana zargin cutar coronavirus ce ta kashe wani likita mai suna Dakta Dominic Essien, kuma malami a tsangayar Tsarin jiki da ke jami’ar Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

Dakta Dominic, ne mamallakin asibitin San Dominique  da ke rukunin gidaje na Ewet a cikin garin Uyo, ya mutu ne a asibitin kwararru na Ibom Multi-Specialist kuma asibitin yana daya daga cikin cibiyar killace masu dauke da cutar Coronavirus a jihar.

Rahotanni na bayyana cewa, marigayin yana dauke da zazzabin da cutar mura da kuma kalubalan shakar nunfashi na tsawan mako guda, hakan yasa ake saka masa na’urar shakar nunfashi a asibitinsa.

Daga bisani ne aka maida shi asibitin kwararru na Ibom Multi-Specialist, don likitocin  da ke kula da masu dauke da cutar COVID-19 su lura da shi, an yi masa gwajin cutar da ke damunsa.

Dakta Dominic, ya mutu kafin a kammala gwaje-gwajen don tabbatar da matsayinsa ko yana dauke da COVID-19.

A cewar shugaban kungiyar likitoci (NMA) reshen jihar Dakta Nsikak Nyoyoko, ya bayyanawa manema labarai ranar Juma’a cewa, har zuwa lokacin da likitan ya rasu ba a kammala tantance abin da ya kashe shi ba.