Da Dumi Dumi

Ana zargin Darakta da abokinsa kan yi wa yarinya ciki a Sakkwato

Ana zargin Daraktan Kudi Ahmad Yahaya Nawawi da wani Habibu Abubakar dukkansu ma’aikata a Hukumar Kula da Tsabtar Birnin Sakkwato, da yi wa wata karamar yarinya mai shekara 14 ciki.

Ana zargi sun hadu da yarinyar ce mai sayar da ruwan leda suka yi lalata da ita a daya daga cikin ofisoshinsu, abin da ya kai ga shigar juna biyu yanzu wata shida.

Wadanda ake zargin sun amince da zargin a bayanan da suka yi daban-daban a ofishin yanki na Hukumar Yaki da Safarar Mutane da Cin Zarafin Yara ta Kasa (NAPTIP).

Sai dai kuma Ahmad Nawawi ya fada wa wakilinmu cewa abin da ake zarginsa kage ne da ’yan siyasa suka shirya masa.

Shi ma Abubakar ya ce zargin kage ne aka yi masa, ya aminta da laifinsa ne a ofishin NAPTIP don sun tilasta masa.

ADVERTISEMENT

Wadda ta raini yarinyar Hajiya Maryam Yusuf ta yi zargin an bai wa mahaifin yarinyar Naira dubu 250 don ya kashe maganar kada ta fita, kuma har ya yi amfani da wani kaso na kudin ya sayi fili.

Malam Muhammadu mahaifin yarinyar ya musanta zargin an ba shi kudi ya janye maganar. Ya fada wa wakilinmu cewa ya karbi Naira dubu 50 ne a wajen mutumin, lokacin da ba ya da lafiya.

Malam Muhammadu ya ce ya janye maganar ce saboda mutunci, ya yarda da kaddara a matsayinsa na Musulmi.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya dauki alkawarin kula da yarinyar da karatunta a yanzu da bayan ta haihu, amma bai fadi matsayarsa kan abin da ke cikin cikinta ba.

Mai rikon yarinyar ta shaida wa wakilinmu cewa iyayen yarinyar sun rabu tun kafin a haife ta, inda mahaifiyarta wadda kanwarta ce ta zauna ta gidanta har ta haifi  yarinyar da abin ya rutsa da ita.

“Mahaifiyar ta rasu bayan ta haife ta dalilin zubar jini da ta samu a lokacin haihuwar. Na so in rike yarinyar a hannuna amma mahaifinta ya ki, tun a lokacin yarinyar take ta safa da marwa tsakanin gidan mahaifinta da gidana, in ka ganta gidana wani abu take so.

“A lokacin ina Nijar wurin kasuwancina dan uwana ya kira ni yake fada min wannan abin bakin ciki da ya faru, saboda haka na dawo gida. Na tafi wajen mahaifinta ya tabbatar min da faruwar lamarin, amma ban ga ya damu ba domin ya riga ya shirya da su. Ni ban gamsu ba domin in har komai ya wuce wace hujja za a ci gaba da tsare ta. Ya ce zai ba da isassun kudi da za a zubar da cikin ya kuma kula da yarinyar, ni zan je ofis na NAPTIP in ganta,” inji ta.

Hajiya Maryam ta ce matsayinta a kan lamarin ya sa ana yi wa rayuwarta barazana saboda ta ki bari lamarin ya mutu.

“Ba zan bari abin ya wuce ba, sun kira ni suka ba ni wasu kudi, amma ban karba ba. Suna yi wa rayuwata barazana,” inji ta.

Kwamadan yanki na Hukumar NAPTIP Abubakar Tabra ya tabbatar da yarinyar na hannunsu, amma ya ki ya ce wani abu kan lamarin domin ya ce ba a ba shi dama ya yi magana da manema labarai kan lamarin ba.

Kwamanda ya kuma ki barin wakilinmu ya zanta da yarinyar.

A lokacin da aka nemi jin ta bakin Mai bai wa Gwamna Aminu Waziri shawara kan Hukumar Tsabtace Birnin Sakkwato, Alhaji Sidi Aliyu Lamido ya ce yana sane da lamarin wadanda ake zargin , kumama’aikatan Ma’aikatar Kudi ne ta Jihar don haka sun rubuta musu domin daukar mataki.

Ko’odinetan Hukumar Kiyaye Hakkin Dan Adam a Sakkwato Barista Hamza Liman ya ce yana sane da lamarin kuma za su bi har karshen lamarin.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya