✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin DPO da kisan ’yar shekara 16 bayan yin lalata da ita a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jahar Katsina na tuhumar wani Jami’inta, wato DPO Sufurtanda Garba Talawai da ke Karamar hukumar Mashi bisa zargin yana da hannu akan…

Rundunar ‘yan sandan Jahar Katsina na tuhumar wani Jami’inta, wato DPO Sufurtanda Garba Talawai da ke Karamar hukumar Mashi bisa zargin yana da hannu akan mutuwar wata yarinya mai suna Rabi Abdullahi mai kimanin shekaru 16 wadda kuma take ‘yar aikin yarinyar shi DPO ce, mai suna Sadiya Alhaji Danyaya.

Shi dai wannan lamari ko tonuwar asirin wannan jami’i ya faru ne bayan kai rahoton tsintar gawar yarinyar da aka yi a cikin daji an jefar. Kamar yadda Aminiya ta samu labari, wani Kansila ne na Karamar hukumar ya kaiwa shi wannan DPO rahoton tsintar ita waccan gawa, wanda nan take Babban Jami’in ya kwashi tawagarsa don zuwa inda gawar take.

Bayan sun dauko gawar ne inda suka kai ta Karamin asibitin da ke cikin garin na Mashi. Bayan zuwan Jami’an ke da wuya tare da mutanan da suka biyo gawar, sai aka yi sa’a, Jami’ar da suka taras ta gane wannan gawa. Nan take ta shaida cewa,”Ai wannan gawar da shi DPO da wani dan sandan da suka kawo ce a jiya.

Rashin amsar gawar daga jami’ar yasa DPO ya koma da ita a cikin motar da suka kawo ta, mai kirar Toyota Carina II wadda aka tabbatar da cewa, ta shi Babban Jami’in ce. Jin wannan bayani daga bakin ita wannan ma’aikaciya ce yasa al’amarin ya canza.

Kamar yadda Aminiya ta kalato, shi dai wannan Jami’i saurayi ne ga uwar dakin ita Rabi, kuma ita Sadiyar ta baiyana cewa, ta shaidawa shi SP Garba batun bacewar Rabi tun ranar 19 ga watan na Yuni 2019 sanadiyar kin amincewa da ganin Rabin da ciki da ita Sadiyar ta yi wanda hakan ya jaza fitar Rabin daga gidan sai fa gawar da ta gani.

Har’ila yau, Aminiya ta samu labarin cewa, ita dai wannan yarinya Rabi marainiya ce wadda ta samu wajen rabawa a wajen ita Sadiya tana yi mata aikin gida.