✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin ma’aurata da kashe dansu a Kurosriba

A farkon makon jiya ne Hukumar ’Yan Sandan Jihar Kkurosriba ta bayyana cewa ta kama wasu ma’aurata da suka kashe dansu dan shekara daya da…

A farkon makon jiya ne Hukumar ’Yan Sandan Jihar Kkurosriba ta bayyana cewa ta kama wasu ma’aurata da suka kashe dansu dan shekara daya da haihuwa.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar na Kurosriba, Hafiz Muhammad Inuwa ya shaida wa Aminiya yadda lamarin ya faru, yana mai cewa, “wasu ma’aurata, Hope Mmeyene Akpan da matar sa Eunice Bassey Akpan ne ake zarginsu da hada baki wajen kashe dansu.”

“An kawo mana kara anan ofishinmu, cewa ga fa wasu ma’aurata da ake zargin sun kasha dansu su da kansu. Kamar yadda makwabta da shaidu suka bayyana mana, cewa sun haifi dansu, sai ya kamu da rashin lafiya suka yi ta jinyarsa, amma sai jinyar ta so ta fi karfinsu, daga nan sai suka yanke shawara suka yi wa yaron wanka suka sanya masa kaya masu kyau, suka dauke shi suka kai can cikin daji, suka kwantar da shi, suka yi tafiyarsu, suka baro shi a can, da haka yaron ya mutu,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “kamar yadda aka shaida mana, bayan makwabta sun ji shiru babu duriyar yaron, sai suka rika bincike suna tambaya, daga bisani aka gano irin matakin da suka dauka, aka kawo mana kararsu,”

“Wannan dalili ya sa bamu yi kasa a gwiwa ba, muka tura jami’anmu suka kamo su, kuma tuni sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa. Yanzu haka suna tsare a hannunmu, muna ci gaba da bincike, kuma da zaran mun kamala, zamu tura su zuwa kotu don fuskantar laifin kisan kai da kuma keta hakkin dan’adam,” a cewarsa.