Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ana zargin mahaifi da yunkurin yanka ’yarsa a Adamawa

Ana zargin wani magidanci mai suna Malam Sa’idu Bello da yunkurin yanka ’yarsa ’yar shekara 10 mai suna Zahra’u Sa’idu.

A hallin yanzu dai Zahra’u na kwance a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Yola, inda likitoci ke kokarin ceto rayuwarta.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gano cewa Malam Sa’idu yana da tarihin tabin hankali wanda hakan ya sanya yake aikata wasu abubuwa da ba su dace ba ga iyalansa.

Mahaifiyar Zahra’u ta ce wannan abu ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar Laraba a gidansu da ke Damare a Karamar Hukumar Yola ta Kudu.

ADVERTISEMENT

Ta bayyana wa wakiliyarmu cewa maigidanta Malam Sa’idu yana da tabin hankali.

Likitan da ke kula da Zahra’u, Dokta Elkana Patrick ya ce yarinyar za ta iya farfadowa domin yankan ya taba wasu sassan wuyarta da bai kamata ba.

Mataimakin Shugaban Asibitin FMC, Dokta Yerima Sulaiman ya bayyana wa Aminiya cewa za su ci gaba da kula da Zahra’u a kyauta domin ceto rayuwarta.

Kakakin ’Yan sandan Jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje ya ce an kama mahaifin inda a halin yanzu ake yi masa wasu tambayoyi da kuma gudanar da bincike game da tabin hankalinsa.